Yanzu: Bayan Shan Matsin Lamba Daga Mata, Majalisa Ta Canja Ra'ayinta Kan Dokar Mata, Za Ta Sake Sabon Kuri'a

Yanzu: Bayan Shan Matsin Lamba Daga Mata, Majalisa Ta Canja Ra'ayinta Kan Dokar Mata, Za Ta Sake Sabon Kuri'a

FCT, Abuja - Majalisar Wakilai na Tarayya ta canja ra'ayinta game da yin garambawul da sassa uku na kundin tsarin mulki da suke da alaka da 'yancin mata na rike wasu mukamai, rahoton Premium Times.

Bayan Zanga-Zanga Da Mata Suka Rika Yi, Majalisa Ta Canja Ra'ayinta Kan Dokar Mata, Za Ta Sake Sabon Kuri'a
Bayan Matsin Lamba Daga Mata, Majalisa Ta Canja Ra'ayinta Kan Dokar Mata, Za Ta Sake Sabon Kuri'a. Hoto: HouseNGR
Asali: Twitter

Hassan Fulata (APC, Jigawa) a ranar Talata ya gabatar da bukatar majalisar da sauya matakin da ta dauka kan wasu kudirori;

1. Kudirin dokar bada izinin zama dan kasa ta hanyar yin rajista.

2. Kudirin dokar bawa mata wasu kejerun mulki da alfarma a shugabancin jam'iyya.

3. Kudirin dokar bada daman zama dan asalin kowanne jiha a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kowawa APC: Gwamna Umahi Ya Yi Martani Kan Ƙwace Masa Ƙujera Da Kotu Ta Yi, Ya Bayyana Matakin Da Zai Ɗauka

Sai dai batun ware wa mata kashi 35 cikin 100 na mukaman gwamnatin tarayya da jihohi ba ya cikin kudirorin da Fulata ya gabatar.

Fatali da kudirorin biyar ya janyo mata sun rika zanga-zanga a kofar Majalisar Tarayya, a yayin da kungiyoyin mata suke kira ga majalisun su sauya ra'ayinsu.

A halin yanzu, akwai mata a kofar shiga Majalisar Tarayyar, suna zanga-zangan fatali da dokokin matan da yan majalisar suka yi.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel