Dalilin da yasa muka yi bikin zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari a Dubai, Matan Gwamnoni

Dalilin da yasa muka yi bikin zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari a Dubai, Matan Gwamnoni

  • Kungiyar matan gwamonin Najeriya ta musanta cewa ta wanki kafa takanas har zuwa Dubai domin kai wa Aisha Buhari kek da furannii
  • Kamar yadda shugabar kungiyar, Bisi Fayemi, uwargidan gwamnan Ekiti ta sanar, ta ce ziyarar aiki suka kai birnin kuma aka yi sa'a ranar ta ratsa
  • A cewarta, wannan zargin bai musu dadi ba kuma babu yadda za a yi babu gaira balle dalili su kwashi kudin kasa domin almubazzaranci

A safiyar Laraba, wani bidiyo yayi yawo a kafafan sada zumuntar zamani inda aka ga wasu daga cikin matan gwamnonin Najeriya suna gabatar da kek ga matar shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari yayin taya murnar zagayowar ranar haihuwar ta, wanda ya gabata a ranar 17 ga watan Fabrairu.

Jim kadan bayan bidiyon ya yadu a yanar gizo, an yada jita-jitar cewa matan gwamnonin Najeriya sun wanki kafa zuwa Dubai musamman don gabatar wa matar shugaban kasan kek da kudin masu biyan haraji.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dakatar da jirgin kai tsaye zuwa Saudiyya na iya hana 'yan Najeriya Umrah a Azumi, CSO

Sai dai bada jimawa ba, bidiyon ya janyo cece-kuce musamman a kafafan sada zumuntar zamani, inda 'yan Najeriya suka caccaki matar shugaban kasar daga ire-iren tsokacin su.

Dalilin da yasa muka yi bikin zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari a Dubai, Matan Gwamnoni
Dalilin da yasa muka yi bikin zagayowar ranar haihuwar Aisha Buhari a Dubai, Matan Gwamnoni. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sai dai Bisi Fayemi, shugabar kungiyar matan gwamnonin Najeriya kuma matar gwamnan jihar Ekiti, ta yi martani a kan batun ta wata takarda da ta fitar a shafinta na Twitter, inda ta musanta cewa, matan gwamnonin basu wanki kafa zuwa Dubai don gabatar wa matar shugaban kasa kek a ranar zagayowar haihuwar ta ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Fayemi ta bada labarin yadda suka kai ziyarar aiki a Dubai, sai yazo dai-dai da ranar zagayowar haihuwar Aisha Buhari saboda haka suka yanke shawarar yi ma ta kyautar ba-zata da kek.

Fayemi ta ce, "An janyo hankalin mu a kan wallafar da aka yi ta yadawa a kafafan sada zumuntar zamani a ranar 1 ga watan Maris 2022, yayin da ake cewa wasu matan gwamnonin Najeriya sun wanki kafa zuwa Dubai don yi wa matar shugaban kasar Najeriya, Dr Aisha Buhari ba-zata a ranar zagayowar haihuwar ta a 17 ga watan Fabrairu 2022.

Kara karanta wannan

Bidiyon matan gwamnoni a ziyarar Aisha Buhari da suka yi Dubai, sun bata kek na bazday

"Don kore shakka, da kuma ra'ayin jama'a, matan gwamnonin Najeriya suna tawagar matar shugaban kasar Najeriya, wacce ta kai ziyarar aiki ga hadaddiyar daular larabawa (UAE).
"Tafiyar ta hada da ziyartar Dubai Expo 2020, da tafiya zuwa Dubai e-learning centre, Dubai Youth Hub da taro tare da kungiyoyi da hukumomi a UAE, wadanda ke da ra'ayin saka hannun jari a bangaren Ilimi, lafiya da fasaha a Afirika, da bada mahimmanci ga mata da matasa masu kananan shekaru."

Ta cigaba da bayyana wa:

"An yi sa'a tafiyar ta zo dai-dai da ranar zagayowar haihuwar ran ta shi dade, Aisha Buhari. A safiyar ranar zagayowar haihuwar ta, wanda ya gabata a 17 ga watan Fabrairu, wakilan matan gwamnonin suka kai mata ziyarar sirri, don gabatar mata da kek da furanni. Bayan gabatarwan na dan takaitaccen lokaci, muka kara gaba don halartar taron da aka shirya na ranar."

Fayemi ta ce, sun yi mamakin ganin yadda aka juya ma'anar labarin bidiyon da yayi yawo a yanar gizo.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Ta ce:

"Maganar gaskiya, ba mu ji dadin yadda aka fassara ziyarar da mukayi ba na cewa mugayen matan gwamnoni sun bar Najeriya kawai don taya murnar zagayowar ranar haihuwar matar shugaban kasa.
"Hakan ba gaskiya bane, kuma mun dauki hakan a matsayin rashin kyautawa. A koda yaushe , shirye muke da bawa mazajen mu karfin guiwa har da matar shugaban kasar mu, kuma ba za mu taba zama musabbabin janyo tozarci garesu da mu ba.
"Abunda ya kamata a fahimta game da ziyarar da muka kai wa hukumomi daban-daban a Dubai da kuma tsokacin da muka samu, na nuni game da bukatar Najeriya ta zuba hannun jari a bangaren Ilimi, kimiyya da fasaha, gami da bawa matasa masu kananan shekaru dama, wadanda sune manyan gobe. Za mu cigaba da bayani a kan wadannan matsalolin, tare da kira ga kara jajircewa a wadannan bangarorin ga shugabannin mu."

Kara karanta wannan

Ango Abdullahi: Dalilin da yasa bana goyon bayan tsarin karba-karba tsakanin shiyyoyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel