Zabtare albashin ma’aikata: Ana gab da shiga sabon yajin aiki a Kano

Zabtare albashin ma’aikata: Ana gab da shiga sabon yajin aiki a Kano

  • Ma'aikata na shirin shiga yajin aiki sakamakon zabtare albashin su da gwamnatin jihar Kano ta yi
  • An ce an samu ragowa a kudaden shiga da asusun tarayya ta tura wa jihohi a watan Fabrairu lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta gaza biyan cikakken albashi ga ma'aikata
  • Hakazalika gwamnatin Kano ta ki yarda da mayarwa ma'aikata da kudaden da aka yanke masu kamar yadda Shugaban kungiyar kwadago na jihar, Kabiru Minjibir, ya bayyana

Kano - Kungiyoyin ma’aikata a Kano na gab da shiga yajin aiki biyo bayan hukuncin gwamnatin jihar na komawa ga albashin da daga watan Fabrairu.

Hakazalika, kungiyoyin ma’aikatan sun yi watsi da bukatar gwamnatin na biyan ma’aikatan kananan hukumomi 18,000 da kuma zabtare albashin ma’aikatan jiha, Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sunaye: Ganduje ya kori jami'ai 4 na gwamnatinsa kan damfarar filaye da bada takardun jabu

Zabtare albashin ma’aikata: Ana gab da shiga sabon yajin aiki a Kano
Zabtare albashin ma’aikata: Ana gab da shiga sabon yajin aiki a Kano Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Shugaban kungiyar kwadago na jihar, Kabiru Minjibir, wanda ya bayyana hakan jim kadan bayan wani taron gaggawa a ranar Alhamis, ya ce kungiyar ta yanke shawarar ne bayan gwamnati ta ki yarda da bukatar dawo da kudaden da aka yanke a albashin.

An samu ragowa a kudaden shiga daga asusun FAAC

Ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta hannun shugabar ma’aikata, Barista Binta Lawal Ahmed, ta fada ma kungiyar ma’aikatan cewa gwamnati ba za ta iya biyan karancin albashi N30,000 ba saboda raguwar kudaden shiga da ta samu daga gwamnatin tarayya a watan Fabrairu.

A cewar Minjibir, shugabar ma’aikatan ta yi ikirarin cewa jihohi 36 da birnin tarayya sun raba naira biliyan 544 a watan Fabrairu sabanin naira biliyan 699 da aka samu a watan da ya gabata, lamarin da ya shafi biyan albashin.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan ta'adda sun ragargaza garinsu sakataren gwamnatin jihar

Minjibir ya ce:

“Muna nesanta kanmu daga hukuncin gwamnati na zabtare albashin ma’aikata, da kuma mayar da albashin ma’aikatan kananan hukumomi zuwa N18,000.
“Tabbass hakan zai shafi yan fansho ma. Shugabar ma’aikata ta kiramu tana sanar mana da cewa raguwa a kudaden shiga na FAAC, shine yasa ba za su iya biyan karamcin albashi ba.
"Sai dai kuma, dukka kungiyoyin kwadago, NLC, TUC, JNC, JCF, NUP da kuma kungiyar ma’aikatan gwamnati a Kano sun yi taro inda suka ba gwamnati zabi, wadanda suka hada da tabbatar da toshe IGR da yin tanadi daga kudaden shiga don kara albashi, da kuma mayarwa ma’aikata da kudaden da aka cire daga albashinsu da zaran kudaden FAAC ya karu zuwa naira biliyan 700. Amma gwamnati ta amince da duk shawarwarin da aka bayar illa na mayar da kason da aka cire daga albashin ma’aikata.”

Minjibir ya kaddamar da cewar NLC ta kai rahoton lamarin ga hedkwatarta na kasa, yayin da take jiran mataki na gaba.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Ya nuna takaici kan yadda gwamnati ta mayar da tsohon albashin, duk da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, tare da karancin man fetur, wanda ke yin illa ga rayuwar ma’aikata.

Leadership ta rahoto cewa ma’aikatan sun koka kan zaftare albashin nasu na Febarairu, saboda watan ya yi nisa har an fice daga cikinsa da karin wasu kwanaki uku zuwa hudu, ga shi wasu sun ciyo bashi sakamakon rashin biyan kudaden kan lokaci don su samu su yi kalaci.

Siyasar Kano: Ganduje ya yi wa Shekarau sabon shagube, ya yabawa aikin Kwankwaso

A wani labarin, mun ji cewa a karshen makon jiya Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya fito, ya na yabon gwamnatin tsohon mai gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso.

A wajen wani taro na jam’iyyar APC mai mulki da aka yi a gidan gwamnatin Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa gwamnatinsa da ta ubangidansa.

Kara karanta wannan

ASUU ta magantu kan sabuwar N1trn da ake yadawa tana bukata daga FG

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta ji a wani bidiyo a shafin Facebook, Mai girma Abdullahi Ganduje ya ce shi da Rabiu Kwankwaso suka canza fasalin jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel