ASUU ta magantu kan sabuwar N1trn da ake yadawa tana bukata daga FG

ASUU ta magantu kan sabuwar N1trn da ake yadawa tana bukata daga FG

  • Kungiyar malamai na jami'o'i, ASUU, ta musanta labarin da ke yawo kan cewa tana bukatar sabuwar N1trn daga FG
  • Shugaban kungiyar na kasa, ya ce suna yajin aiki ne kan N1.3trn da FG ta musu alkawarin za ta dinga biya N200b duk shekara amma ta ki
  • A cewarsa, za a dinga amfani da kudaden ne wurin gyaran jami'o'in gwamnati, duk da gwamnatin ta hana su kudadensu da suke bin ta

Kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU, ta musanta rade-radin da ke yawo kan cewa suna bukatar sabuwar tiriliyan daya daga gwamnatin tarayya a matsayin sharadin janye yajin aiki.

TheCable ta ruwaito cewa, ASUU ta fada yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairu bayan kwanaki biyu da suka kwashe suna zantawa a tsakanin shugabannin kungiyar.

Kara karanta wannan

Matsafa sun yi luguden wuta kan masu makoki, sun yi fatali gawar mamacin

Kungiyar ta zargi gwamnati da tozarta yarjejeniyarsu wacce ta sa suka janye yajin aikin da suka yi a shekarar 2020.

ASUU ta magantu kan sabuwar N1trn da ake yadawa tana bukata daga FG
ASUU ta magantu kan sabuwar N1trn da ake yadawa tana bukata daga FG. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

ASUU ta kara da cewa ta kara fadawa yajin aiki ne sakamakon halayyar gwamnati kan sasancin da suka nema a fannin albashinsu da alawus dinsu tare da karbar tsarin biyan albashi na University Transparency Accountability Solution (UTAS).

Malaman sun fusata ne sakamakon rashin fitar da kudin farfado da jami'o'in gwamnati da kuma biyansu kudaden karin girma da suke bi.

Sauran bukatun sun hada da sasanci kan yarjejeniyar ASUU da gwamnatin tarayya na 2009 da kuma rashin daidaito na tsarin biyan albashin Integrated Personnel and Payroll Information System (IPPIS).

Tuni gwamnatin tarayya ke ta ganawa da kungiyar domin samo hanyar da za su janye yajin aikin, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta sa labule da kungiyar ASUU a Abuja

Emmanuel Osodeke, shugaban ASUU yayin zantawa da TheCable a ranar Lahadi, ya bayyana damuwarsa kan yadda gwamnati ta ki hobbasa kan yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

A yayin da aka tambaye shi kan rade-radin da ke yawo na sabuwar bukatar kudi da suka mika, Osodeke ya ce babu gaskiya a zancen.

"Mun bayyana inda muka tsaya a taron. Babu wanda ya bukaci N1 tiriliyan. Ba mu cika martani kan rade-radi ba. Abinda muke bukata na zuwa ne bayan gwamnati ta amince za ta kashe N1.3 tiriliyan a 2009," shugaban ASUU din ya kara da cewa.
"Za a dinga biyan N200 biliyan a kowacce shekara na tsawon shekara biyar ko shida. Ba su yi hakan ba, abinda muke bukata kenan a yanzu."

ASUU ga FG: Ba za ku taba samun kwanciyar hankali ba, har sai mun sasanta

A wani labari na daban, kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i, ASUU, a jiya ta sanar da gwamnatin tarayya cewa ba za ta samu kwanciyar hankali ba har sai ta sasanta da su kan halin da ilimin jami'o'i ke ciki.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Abin da APC ta fada sa’ilin da ASUU ta yi dogon yajin-aiki a mulkin Jonathan

A wata zantawa da manema labarai a Awka, shugaban ASUU na jami'ar Nnamdi Azikiwe, Comrade Stephen Ofoaror ya ce ya gane yadda ake neman barazana ga zaman lafiyan kasar.

Vanguard ta ruwaito cewa, inda ya ja kunne a kan bakar guguwar da ta taso sanadiyyar gazawa wurin cika alkawarin da gwamnatin tarayya ta dauka na girmama yarjejeniyar da ta yi da ASUU a ranar 23 ga watan Disamba, 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel