Sunaye: Ganduje ya kori jami'ai 4 na gwamnatinsa kan damfarar filaye da bada takardun jabu

Sunaye: Ganduje ya kori jami'ai 4 na gwamnatinsa kan damfarar filaye da bada takardun jabu

  • Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kori maa'aikata hudu na gwamnatinsa kan kama su da laifin damfara
  • Kamar yadda kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya fitar a wata takarda, an yi bincike an kama su da laifin bada takardun bogi
  • Ya ja kunnen ma'aikatan gwamnati inda yace hakan ya zama izina garesu kuma sauran su kasance masu gaskiya da rikon amana

Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kori ma'aikatan gwamnati hudu da ke aiki a karkashin ofishin hukumar kula da filaye kan laifin siyar da kadarori, bada takardun bogi da kuma bayanan karya.

Premium Times ta ruwaito cewa, a wata takarda da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya sa hannu a ranar Talata, ya ce korarrun ma'aikatan sune:

Abdulmuminu Usman Magami,

Abdullahi Nuhu Idris

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan ta'adda sun ragargaza garinsu sakataren gwamnatin jihar

Audu Abba Aliyu

Baba Audu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sunaye: Ganduje ya kori jami'ai 4 na gwamnatinsa kan damfarar filaye da bada takardun jabu
Sunaye: Ganduje ya kori jami'ai 4 na gwamnatinsa kan damfarar filaye da bada takardun jabu. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Garba wanda ya ce an kori jami'an gwamnatin saboda bukatar da kwamitin da gwamnati ta kafa ya mika, an gano cewa sun aikata laifin bayan korafin da aka mika a kansu.

Ya yi bayanin cewa, korarsu ya yi daidai da dokar aikin gwamnati ta 04406 inda ya kara da cewa wannan hukuncin an yanke shi ne domin ya kasance izina ga wasu.

Kwamishinan ya ja kunnen cewa, gwamnatin jihar ba za ta lamunci rashin da'a ba daga kowanne ma'aikacinta.

"A don haka, ana tsammanin dukkan ma'aikatan gwamnatin za su sauke hakkin da ke kansu cike da gaskiya da amana, jajircewa kuma cike da biyayya ga dokokin ayyukan gwamnati," yace.

Kano: 'Yan sanda sun damke matashin da ya yaga Qur'ani tare da taka shi

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

A wani labari na daban, wani matashin maigadi wanda har yanzu ba a san sunansa ba, ya na hannun hukumar 'yan sanda ta jihar Kano kan zarginsa da ake yi da yaga Qur'ani tare da take wani sashinsa.

Wanda ake zargin, ya kubuta daga babbaka shi da ranshi da jama'ar yankin Kuntau a birnin Kano suka yi niyya bayan isar jami'an hukumar Hisbah wurin.

Daga bisani jami'an Hisbah sun mika shi hannun 'yan sanda kuma a halin yanzu an tsare shi inda ake cigaba da bincike. Wani dan uwan mamallakin gidan da matashin ke gadi mai suna Sunusi Ashiru, ya sanarwa da Daily Trust cewa an tabbatar masa da kyar matashin ya kubuta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel