Da Ɗuminsa: Buhari Ya Naɗa Magajin Farfesa Sulaiman Bogoro A TETFund

Da Ɗuminsa: Buhari Ya Naɗa Magajin Farfesa Sulaiman Bogoro A TETFund

  • Shugaban kasa Muhummadu Buhari ya amince da nada Arc S.T. Echono a matsayin sabon shugaban hukumar TETFund
  • Echono, zai karba aiki ne daga hannun Farfesa Sulaiman Elias Bogoro wanda wa'adinsa na shekara biyar zai kare a ranar 18 ga watan Maris na 2022
  • Kafin nadinsa, Echono ya yi aiki a matsayin sakataren dindindin a Ma'aikatar Ilimi ta Tarayyar kuma mamba ne a kwamitin amintattu na TETFund ds

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Arc S.T. Echono a matsayin sabon shugaban hukumar bayar da tallafi ga manyan makarantu ta Najeriya wato TETFUND.

Echono, tsohon sakataren dindindin na ma'aikatar ilimi, zai maye gurbin Farfesa Sulaiman Elias Bogoro ne, wanda wa'adinsa na shekara biyar zai kare a ranar 18 ga watan Maris na 2022, rahoton Daily Trust.

Da Ɗuminsa: Buhari Ya Naɗa Magajin Farfesa Sulaiman Bogoro A TETFund
Da Ɗuminsa: Buhari Ya Naɗa Sakatare a TETFund. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Direktan sashin watsa labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi ta tarayya, Ben Bem Goong ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar.

Sanarwar ta ce:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Arc Sunday S.T. Echono a matsayin sabon sakataren Asusun Ilimi na manyan makarantu, TETFund. Zai maye gurbin Farfesa Sulaiman Elias Bogoro wanda wa'adinsa na shekara biyar zai kare a ranar 18 ga watan Maris na 2022."

Sanarwar ta bayyana Echono a matsayin kwararren ma'aikacin gwamnati wanda ƙwarewarsa a bangarorin ayyuka, kasuwanci, mulki, kimiyya da fasahar sadarwa zamani da ilimi za su taimaka masa wurin aiki.

Kafin nadinsa, ya yi aiki a matsayin sakataren dindindin a Ma'aikatar Ilimi ta Tarayyar kuma mamba ne a kwamitin amintattu na TETFund da wasu mukaman a kasa.

Saurari ƙarin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel