Yadda matan Gwamnoni su ka fusata mutane da suka kai wa Aisha Buhari ‘cake’ har Dubai

Yadda matan Gwamnoni su ka fusata mutane da suka kai wa Aisha Buhari ‘cake’ har Dubai

  • Mun tattaro martanin jama’a yayin da matan Gwamnonin jihohi suka tashi daga Najeriya, suka je Dubai
  • Iyalan gwamnonin jihohin kasar sun kai wa matar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari ‘cake’ kwanaki
  • A kan lamarin, Legit.ng Hausa ta dauko ra’ayin wasu masu amfani da shafin Facebook da kuma Twitter
  • Watakila ba kwanan nan abin ya faru ba domin a watan Fubrairu ne Aisha Buhari ta cika shekara 51
“Ta ina ma za a fara sharhin wannan? Ko ta ina dai, tsarin shugabancin Najeriya ya sukurkuce, ba ya yi wa kowa aiki sai shugabanni, bai taba taimakon talakawa ba. Ya wajaba ayi wa salon shugabancin mu garambawul.”

- Ayo Sogunro

Kai Allah, wannan abin kunya ne.

- Najeeb Wali

Buhari ya na Landan domin a duba lafiyarsa, matan gwamnoni su na Dubai domin su kai wa Aisha Buhari ‘cake’. Wahalar man fetur yana ta karuwa, lita ta kai N300 kuma ASUU su na yajin-aiki…”

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

- First Lady Ship

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wayyo Jonathan?

"Muhammad Buhari yana UK, mai dakinsa, Aisha Buhari ta na Dubai domin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta. Mutanen Najeriya su na bin layin mai domin sayen fetur duk da mu na da arzikin danyen mai. Kuma mu ka so ayi waje da Jonathan kan abin da bai kai wannan ba."

- Sarki Waspapping

“Ka yi tunani da a ce lokacin Jonathan aka yi wannan aikin. Buhari da iyalinsa sun damfari mutanen Najeriya da kyau. Abin da ya fi wannan muni, shi ne akwai wadanda suke ganin babu komai a hakan…Duk da haka akwai wanda a shirye suke da su kare Buhari da jininsu”

- I2Much4Dem

Aisha Buhari da ‘cake'
Aisha Buhari da Mai gidanta Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Ban da Uwargidar gwamnan Oyo

"Ba za ka samu mai dakin gwamnan Oyo a irin wannan taron ba. Wadannan matan su na batar da dukiyoyin jihohinsu ne. Abin ban dariya, matar da suke tayawa murna uwargidar shugaban kasa ce wanda take zama a wajen Najeriya.”

Kara karanta wannan

Duka Gwamnonin APC za su yi zaman musamman domin dinke sabuwar baraka kan mukamai

- Sodiq Tode

"Ba za ka iya ganin uwargidar jihar Oyo, Injiniya Tamunominni Makinde a irin wannan abubuwa ba. Makinde ba ya goyon bayan fadanci."

- Francis Adeboye

“Idan matar Wike ta nemi yin wannan, dakarun musamman da aka kafa ba za su bar ta, ta dawo jihar ba. Wannan kyakkyawar matar ta fi karfin wannan shirmen."

- Sexy Oma

"A fagen yaki, uwargidar shugaban Ukraine, Olena Zelenska ta ki barin mai gidanta. Ta na nema masa goyon baya. Amma a Najeriya, Aisha Buhari ta tsere zuwa Dubai a lokacin da kasar nan ta ke lafiya lau, ta bar al’umma a hannun Buhari…"

- OG Kuku

Ana surutu a Facebook

"An ce Uwar gidar shugaban Najeriya ta na shanawa na bikin ranar zagayowar haihuwarta; mai gidanta ba ya nan; litar man fetur ya kai N240. Najeriya kenan!"

- Muhammad Hashim Suleiman

"Nayi asara idan ban zabi (Yele) Sowore ba, kai jama’a!"

- Sho Sho

"Ina fatan matar Wike ba ta je ba dai!"

Kara karanta wannan

Ministoci da Shugabannin Gwamnatin da ke daf da asarar kujerunsu a sabuwar dokar zabe

- Gloria West

Asali: Legit.ng

Online view pixel