'Karin Bayani: NDLEA Ta Yi Karar Abba Kyari Da Wasu Mutane 6 a Kotu, Ana Tuhumarsu Da Laifuka 8

'Karin Bayani: NDLEA Ta Yi Karar Abba Kyari Da Wasu Mutane 6 a Kotu, Ana Tuhumarsu Da Laifuka 8

  • A yayin da Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya bada umurnin a mika dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari ga Amurka don amsa tambayoyi
  • Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta maka Abba Kyarin da wasu mutane 6 a babban kotun Abuja tana tuhumarsu da laifuka takwas
  • Ana tuhumar Kyari da wasu yan sanda hudu yan tawagar IRT ne da laifun safarar hodar iblis da mallakarta ba bisa ka'ida ba yayin da sauran mutane biyu ake tuhumarsu da shigo da kwaya Najeriya

FCT, Abuja - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, a ranar Alhamis, ta shigar da kara kan dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP, Abba Kyari, da wasu mutane shida kan zarginsu da hannu a safarar miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan

Hotuna: Shugaba Buhari ya dira birnin Nairobi, inda daga nan zai tafi Landan ganin Likita

Bayan Kyari, sauran mutanen da aka yi karar a babban kotun tarayya, Abuja sun hada da yan tawagar yan sanda na IRT; ACP Sunday J. Ubia, ASP Bawa James, Insp. Simon Agirigba da Insp. John Nuhu.

Yanzu-Yanzu: NDLEA Ta Yi Karar Abba Kyari Da Wasu Mutane 6 a Kotu, Ana Tuhumarsu Da Laifuka 8
NDLEA Ta Yi Karar Abba Kyari Da Wasu Mutane 6 a Kotu, Ana Tuhumarsu Da Laifuka 8. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Sauran biyun kuma wasu da ake zargin masu safarar kwaya ne da aka kama a filin tashin jirage na Akanu Ibiam a Enugu, Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne, rahoton Vanguard.

NDLEA, a karar da ta shigar ta hannun tawagar lauyoyinta karkashin Mr Joseph Sunday, ta zargi DCP Kyari da wasu yan sanda hudu da laifin hadin baki, dakile bincike da dillancin hodar koken mai nauyin kilogram 17.55.

Hakazalika, ta yi ikirarin cewa Kyari da jami'ansa, wanda a yanzu suna tsare, sun kuma yi ta'amulli da hodar koken ba bisa ka'ida ba wanda nauyinsa ya kai kilogram 21.25.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari, ta ce ba za a bada belinsa ba

Su kuma Umeibe da Ezenwanne an zarge su ne da hadin baki wurin safarar hodar koken mai nauyin kilogram 21.35 zuwa Najeriya kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya amince a tura Kyari Amurka

NDLEA sun shigar da karar ne kwana guda bayan Antoni Janar kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, SAN, ya amince da bukatar tura Kyari Amurka don ya amsa tambayoyi kan alakarsa da dan damfarar intanet, Ramon Abbas, wato Hushpuppi.

A cikin takardar na tura DCP Abba Kyari zuwa Amurka da Malami ya gabatar a kotu, ya yi ikirarin babu wani tuhuma da ake yi wa Kyari a Najeriya.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel