Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine

Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine

  • Wasu 'yan Najeriya sun nuna sha'awar taimakawa kasar Ukraine ta shawo kan mamayar da sojojin Rasha suka yi wa kasar a makon jiya
  • Wasu matasa 'yan Najeriya masu sha'awar taimakawa Ukraine sun yi wa ofishin jakadancin Ukraine kawanya a babban birnin tarayya Abuja
  • Haka lamarin yake a kasashe da dama kamar yadda 'yan Burtaniya, Amurkawa da kuma 'yan Kanada suma suka nuna sha'awar taimakawa Ukraine

Kimanin matasa 115 ‘yan Najeriya ne, a ranar Talata, 1 ga watan Maris, suka nuna sha'awar shiga yakin kasar Ukraine da Rasha.

Matasan da suka yiwa ofishin jakadancin Ukraine da ke Abuja babban birnin Najeriya kawanya, sun kuma sanya sunayensu a cikin wata rajista da ofishin jakadancin ya bayar.

An amsa kiran shugaban Ukraine
Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine | Hoto: sawahpress.com
Asali: UGC

Jaridar Guardian ta rawaito cewa jami'an ofishin jakadancin sun dakile yunkurin daukar hotunan mutane a bakin ofishin.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraine: Abubuwa 12 da suka faru bayan tattaunawar sulhun Rasha da Ukraine

Sakatare na biyu na ofishin jakadancin Ukraine, Bohdan Soltys, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa har yanzu ba a dauki matakin da ya dace ba.

Ku zo ku taya mu yaki: Shugaban Ukraine na neman sojoji daga Najeriya da sauran kasashe

A tun farko, kasar Ukraine ta ce tana maraba da mayaka daga kasashen duniya da ke da sha'awar yaki don kare Ukraine a ci gaba da mamayar da sojojin Rasha ke yiwa kasar a halin yanzu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Volodymyr Zelenskyy, shugaban kasar Ukraine ya rattaba hannu kan wata doka ta wani dan lokaci don tabbatar da faruwar hakan.

Dokar ta dage bukatar takardun shiga kasar ta Ukraine ga duk wani dan kasar waje da ke son shiga rundunar sojin kasa da kasa ta Ukraine, in ji Aljazeera.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Dokar Zelenskyy ta fara aiki ne a ranar Talata kuma za ta ci gaba da aiki muddin dokar soja ta kasance a kasar.

Yakin Rasha da Ukraine: Abubuwa 12 da suka faru bayan tattaunawar sulhun Rasha da Ukraine

A wani labarin, wakilan Rasha da Ukraine a ranar Litinin 28 ga watan Fabrairu sun fara tattaunawar zaman lafiya tun bayan da shugaba Vladimir Putin ya umarci dakarunsa su mamaye Ukraine a makon jiya. Wakilan kasashen biyu sun gana a kan iyakar Belarus da Ukraine don tattaunawa ta farko.

An tattaro cewa babban makasudin taron shine tattauna batun tsagaita wuta da kuma kawo karshen yaki akan Ukraine.

Legit.ng ta tattaro muku abubuwan da suka faru bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin kasahen biyu kamar yadda The Asean Post ta ruwaito:

Asali: Legit.ng

Online view pixel