Yakin Rasha da Ukraine: Abubuwa 12 da suka faru bayan tattaunawar sulhun Rasha da Ukraine

Yakin Rasha da Ukraine: Abubuwa 12 da suka faru bayan tattaunawar sulhun Rasha da Ukraine

  • Yunkurin mamaye kasar Ukraine da sojojin Rasha karkashin jagorancin Vladimir Putin suka yi na ci gaba da tayar da hankula a tsakanin shugabannin kasashen duniya
  • Tuni dai kasashe daban-daban suka bayyana shirin kakaba takunkumi kan gwamnatin kasar Rasha bisa kokarin mamaye Ukraine
  • A daidai wannan lokaci na takunkumi, wakilan Rasha da na Ukraine a ranar Litinin, 28 ga Fabrairu, sun fara tattaunawar sulhu

Wakilan Rasha da Ukraine a ranar Litinin 28 ga watan Fabrairu sun fara tattaunawar zaman lafiya tun bayan da shugaba Vladimir Putin ya umarci dakarunsa su mamaye Ukraine a makon jiya.

Wakilan kasashen biyu sun gana a kan iyakar Belarus da Ukraine don tattaunawa ta farko. An tattaro cewa babban makasudin taron shine tattauna batun tsagaita wuta da kuma kawo karshen yaki akan Ukraine.

Abubuwan da suka biyo bayan tattaunawar sulhu
Sulhun Rasha da Ukraine: Batutuwa 12 da suka biyo bayan tattaunawar sulhu tsakanin kasashen biyu | Hoto: sawahpress.com
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro muku abubuwan da suka faru bayan tattaunawar zaman lafiya tsakanin kasahen biyu kamar yadda The Asean Post ta ruwaito:

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

1. Shirin 'ko ta kwana' daga mazauna a Arewacin Kyiv

Hotunan tauraron dan adam sun nuna wani katafaren gungu na soji da ke kai komo a Arewacin Kyiv babban birnin kasar Ukraine, inda mazauna yankin suka nuna kwarin gwiwa da shirin ko ta kwana kan harin Rasha.

Sojojin Rasha sun shaidawa mazauna yankin cewa za su iya barin babban birnin kasar ta wata babbar hanya da ke zuwa Kudu yayin da suke nuna alamun hare-hare a kan fararen hula.

2. 'Yan gudun hijira

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutane 520,000 ne suka tsere daga Ukraine a cikin kwanaki biyar da suka gabata, tare da wasu dubun dubatan da suka rasa matsugunansu a cikin kasar, in ji rahoton NDTV.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraine: An kammala zama na farko don sulhunta tsakanin kasashen biyu

A cewar Ukraine, fararen hula 52 ne suka mutu, ciki har da yara 14, tun bayan da Rasha ta fara kai farmakin kan 'yan kasar a ranar Alhamis.

3. Laifin cin zarafin bil'adama da tayar da yaki

Mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa Karim Khan ya ce yana gudanar da bincike kan halin da ake ciki a Ukraine, yana mai cewa akwai “tushen” da za a yi imani da cewa “an aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama” tun daga shekarar 2014.

4. Turkiyya ta toshe jigilar jiragen ruwan yaki

Turkiyya ta toshe jiragen ruwan yaki daga mashigar Bosphorus da ta Dardanelles, tare da takaita zirga-zirgar jiragen ruwan Rasha da sauran jiragen ruwa daidai da yarjejeniyar 1936.

5. Za a ci gaba da tattaunawa a nan gaba

Masu shiga tsakani daga Ukraine da Rasha sun kawo karshen tattaunawar farko ba tare da cimma wata matsaya ta zaman lafiya ba. Bangarorin biyu sun amince da gudanar da zagaye na biyu "nan ba da jimawa ba".

Kara karanta wannan

An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

EU ta kara da wasu kawayen Putin cikin jerin wadanda ta sanya wa takunkumi, wadanda suka hada da mai magana da yawun Kremlin Dmitry Peskov da shugabanni irinsu Igor Sechin, Alisher Usmanov, Petr Aven da Mikhail Fridman.

6. Bukatun Putin

A rahotannin da suka gabata, shugaban Rasha Vladimir Putin ya bukaci da "rage karfin soja da kange" Ukraine daga shiga jerin kasashen Yamma, kana da amincewa da ware yankin Crimea.

7. Gimtse kafafen sada zumunta

Twitter da Facebook sun yi wani yunkuri na gimtse kafafen yada labaran da ke da alaka da gwamnatin Rasha ta intanet.

8. Haramci daga FIFA

An kori Rasha daga gasar cin kofin duniya ta 2022 kuma an kuma dakatar da kungiyoyinta daga duk wasu wasannin kwallon kafa na kasa da kasa har sai baba ta gani, a cewar FIFA da UEFA.

Hakazalika, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya kuma bukaci kungiyoyin wasanni da su haramtawa 'yan wasan Rasha da Belarus halartar wasanni domin nuna adawa da mamayar Rasha a Ukraine.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Belarus ta shiga yakin Rasha, tana shirin danna dakarunta cikin Ukraine

9. An kori 'yan Rasha daga Amurka

Amurka ta kori mambobin tawagar Rasha 12 daga Amurka saboda kasancewarsu "ma'aikatan leken asiri" na kasar Rasha.

10. Tsoron yakin nukiliya

Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya, IAEA, ya nuna "damuwa sosai" cewa sojojin Rasha da suka mamaye Ukraine na aiki kusa da Zaporizhzhia, tashar nukiliya mafi girma a Ukraine.

11. Haramta fina-finan Hollywood

Kamfanonin fina-finai na Disney da Sony sun dakatar da fitar da fina-finansu a gidajen sinima na Rasha saboda mamayar da suka yi a Ukraine.

12. Karin takunkumi

Amurka da Kanada sun haramta duk wata mu'amala da babban bankin Rasha a cikin wani takunkumin da ba a taba ganin irinta ba.

Ku zo ku taya mu yaki: Shugaban Ukraine na neman sojoji daga Najeriya da sauran kasashe

A wani labarin, ana maraba da mayaka daga kasashen duniya da ke da sha'awar yaki don kare Ukraine a ci gaba da mamayar da sojojin Rasha ke yiwa kasar a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Ukraine da Rasha za su yi zaman tattaunawar sulhu, an fadi inda za a gana

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Volodymyr Zelenskyy, shugaban kasar Ukraine ya rattaba hannu kan wata doka ta wani dan lokaci don tabbatar da faruwar hakan.

Dokar ta dage bukatar takardun shiga kasar ta Ukraine ga duk wani dan kasar waje da ke son shiga rundunar sojin kasa da kasa ta Ukraine, in ji Aljazeera.

Asali: Legit.ng

Online view pixel