Ku zo ku taya mu yaki: Shugaban Ukraine na neman sojoji daga Najeriya da sauran kasashe

Ku zo ku taya mu yaki: Shugaban Ukraine na neman sojoji daga Najeriya da sauran kasashe

  • Volodymyr Zelenskyy ya yi kiran neman 'yan sa kai da ke shirye su yi yaki don kare Ukraine daga ko'ina suke a fadin duniya
  • Sakamakon haka, shugaban na Ukraine ya rattaba hannu kan wata doka ta wani dan lokaci da ta dage sharuddan shiga kasar ga duk wani bakon da ke son shiga aikin tsaron Ukraine
  • Dokar ta Zelenskyy ta fara aiki ne a ranar Talata kuma za ta ci gaba da aiki muddin dokar soja ta kasance a kasar

Kiev, Ukraine - Ana maraba da mayaka daga kasashen duniya da ke da sha'awar yaki don kare Ukraine a ci gaba da mamayar da sojojin Rasha ke yiwa kasar a halin yanzu.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Volodymyr Zelenskyy, shugaban kasar Ukraine ya rattaba hannu kan wata doka ta wani dan lokaci don tabbatar da faruwar hakan.

Kara karanta wannan

An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

Shugaban kasar Ukraine na neman sojoji daga kasashen waje
Ku zo ku taya mu yaki: Shugaban Ukraine na neman sojoji daga Najeriya da sauran kasashe | Hoto: sawahpress.com
Asali: UGC

Dokar ta dage bukatar takardun shiga kasar ta Ukraine ga duk wani dan kasar waje da ke son shiga rundunar sojin kasa da kasa ta Ukraine, in ji Aljazeera.

Dokar Zelenskyy ta fara aiki ne a ranar Talata kuma za ta ci gaba da aiki muddin dokar soja ta kasance a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku tuna cewa rahoton da Daily Mail ta fitar ya nuna cewa makaman roka na Rasha sun yi luguden wuta kan biranen Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine a ranar Litinin 28 ga watan Fabrairu.

Hukumomi a birnin Kiev sun tabbatar da cewa an kashe fararen hula da dama tare da jikkata wasu daruruwa a wani harin da aka bayyana a matsayin daya daga cikin hare-hare mafi muni tun bayan fara yakin kwanaki biyar da suka gabata.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: 'Yan Najeriya sun samu mafaka a kasashe biyu da ke makwabtaka da Ukraine

Yakin Rasha da Ukraine: An kammala zama na farko don sulhunta tsakanin kasashen biyu

A wani labarin, an kawo karshen tattaunawar zaman lafiya ta farko tsakanin tawagogin Ukraine da Rasha da aka yi a kan iyakar kasar da Belarus a yau Litinin.

Ba a bayyana sakamakon tattaunawar ba. Tattaunawar ta dauki sa'o'i da yawa kuma an raba shi gida biyu, in ji Jonah Hull na kafar labarai ta Al Jazeera, yana mai karawa da cewa tsayin taron ya nuna cewa akwai abubuwan da za a yi magana akansu.

Bayan tattaunawar, masu shiga tsakani daga Ukraine da Rasha za su koma babban birnin kasashensu domin tuntubar juna.

Shugaban tawagar sulhu Rasha, Vladimir Medinsky, ya ce bangarorin biyu "sun amince da ci gaba da tattaunawar."

Asali: Legit.ng

Online view pixel