Yakin Rasha da Ukraine: An kammala zama na farko don sulhunta tsakanin kasashen biyu

Yakin Rasha da Ukraine: An kammala zama na farko don sulhunta tsakanin kasashen biyu

  • A yau ne aka yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha a kan iyakar Belarus da ke makwabtaka
  • Ya zuwa yanzu, rahotanni basu bayyana matsayar da aka ajiye ba, amma an ce za a sake zama don tsayar da magana
  • Bangarori biyun sun amince da wasu batutuwa inji rahotannin da muke samu daga majiyoyi masu tushe

Ukraine - An kawo karshen tattaunawar zaman lafiya ta farko tsakanin tawagogin Ukraine da Rasha da aka yi a kan iyakar kasar da Belarus a yau Litinin.

Ba a bayyana sakamakon tattaunawar ba. Tattaunawar ta dauki sa'o'i da yawa kuma an raba shi gida biyu, in ji Jonah Hull na kafar labarai ta Al Jazeera, yana mai karawa da cewa tsayin taron ya nuna cewa akwai abubuwan da za a yi magana akansu.

Kara karanta wannan

An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

Yankin Ukraine da Rasha: An tattauna da juna
Yakin Rasha da Ukraine: An kammala zama na farko don sulhunta tsakanin kasashen biyu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bayan tattaunawar, masu shiga tsakani daga Ukraine da Rasha za su koma babban birnin kasashensu domin tuntubar juna.

Shugaban tawagar sulhu Rasha, Vladimir Medinsky, ya ce bangarorin biyu "sun amince da ci gaba da tattaunawar."

Wani dan majalisar dokokin Ukraine ya fada wa Fox News cewa:

“Tattaunawar ta zo karshe, wakilai sun gano batutuwan da za su amince da su a gaba, yanzu za su koma manyan biranensu domin tuntubar juna, an yi tataunawa har sau 3.
"Ya zuwa yanzu babu wani sakamako mai ma'ana amma sun amince su sake haduwa a kan iyakar Belarus da Poland bayan tuntubar juna."

An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

A wani labarin na daban, rahoton da muka samo daga jaridar Independent ta kasar Burtaniya ya ce, kasar Belarus za ta karbi bakuncin tattaunawar zaman lafiya ta farko tsakanin Ukraine da Rasha a kan iyakarta, kwanaki biyar bayan da Vladimir Putin ya farmaki Ukraine.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Ukraine da Rasha za su yi zaman tattaunawar sulhu, an fadi inda za a gana

Wannan batu na zuwa ne a yau Litinin, 28 ga watan Fabrairu, kasa da mako kenan da mamayar Rasha a kasar Ukraine.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwannin kasar Rasha suka fara fuskantar dakansu, inda farashin Ruble na Rasha ya yi kasa a tarihi, sannan bude kasuwar hada-hadar hannayen jari ya jinkirta har zuwa tsakar rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel