Daga karshe: Ukraine da Rasha za su yi zaman tattaunawar sulhu, an fadi inda za a gana

Daga karshe: Ukraine da Rasha za su yi zaman tattaunawar sulhu, an fadi inda za a gana

  • Yayin da duniya ta dauki dumi tun bayan da rikici ya barke tsakanin Ukraine da Rasha, ana kyautata zaton samun mafita nan kusa
  • Kasar Ukraine ta bayyana amincewa da tattaunawa da kasar Rasha domin samun mafita da sulhu kan rikicin da ake ciki
  • Tuni an shirya, har an bayyana wurin da za a yi wannan tattaunawar da bangarorin biyu suka amince za su yi nan kusa

Ukraine - Rahotannin da ke shigowa daga kasashen ketare sun bayyana cewa, kasar Ukraine ta bayyana amincewa da tattaunawa da kasar Rasha yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubalen hare-hare tsakanin kasashen biyu.

Tashar watsa labarai ta AlJazeera ta rahoto cewa, shugaban kasar Ukraine ya ce kasarsa a shirye take don tattaunawa da Rasha, amma ba a yankin Belarus ba.

Shugaban Ukraine ya amince a yi sulhu
Daga karshe: Ukraine da Rasha za su yi zaman tattaunawar sulhu, an fadi inda za a gana | Hoto: sawahpress.com
Asali: UGC

Kalaman shugaba Zelenskyy na zuwa ne bayan da fadar Kremlin ta ce tawagarta a shirye take ta gana da jami'an Ukraine a birnin Gomel na Belarus domin a caccaka tsinke.

Rasha dai ta dasa dubunnan dakaru a Belarus kafin ta daga bisani ta mamaye Ukraine, yayin da kasar ta zargi birnin Moscow da amfani da kasar a matsayin matattarar mamayar da ta yi.

An hada wakilan tattaunawar sulhu

A wani rahoton DW da ke tabbatar da batu makamancin na sama, an ce shugaban kasar na Ukraine ya amince da fara tattaunawar sulhun da kasar Rasha, kamar yadda ofishinsa ya bayyana a yau Lahadi.

Rahoton ya ce, bayan wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, ofishin Zelenskyy ya ce a shirye ya ke ya aika da tawaga zuwa tattaunawar a kan iyakar Belarus da Ukraine kusa da kogin Pripyat.

Tattaunawar dai za ta kasance ta farko ne tun bayan da Rasha ta dumfari Ukraine. Mataimakan shugaba Zelenskyy sun ce za a yi tattaunawar ba tare da wani sharadi ba.

An nakato Zelenskyy na cewa:

"Mun amince cewa tawagar Ukraine za ta gana da tawagar Rasha ba tare da wani sharadi ba a kan iyakar Ukraine da Belarus, kusa da kogin Pripyat."

Shugaban Belarus Lukashenko ya tabbatar wa Zelensky cewa:

"Dukkan jirage, jirage masu saukar ungulu da makamai masu linzami da aka jibge a yankin Belarus za su ci gaba da kasancewa a wurin yayin jigilar, tattaunawar da kuma dawowar tawagar Ukraine."

Ukraine: Ba bu abin da zai faru da 'yan Najeriya, Rasha ta fada wa FG

A wani labarin na daban, jakadan kasar Rasha a Najeriya, Alexei Shebarshin, ya tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa ‘yan Najeriya baza su cutu ba a rikicin da ke ta ballewa tsakanin kasar Rasha da Ukraine, The Punch ta ruwaito.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya samu damar ganawar sirri da jakadan ya shaida wa Shebarshin cewa Najeriya kawar Rasha ce.

A cewar Onyeama, yayin tattaunawa da Shebarshin ya sanar da shi cewa Najeriya baza ta lamunci cin zarafin kasa da kasa ba daga wata kasar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, kasar da ke da jakada a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel