Baje kolin Kaduna: Kamfanin takin Dangote zai gudanar da shiri tsakaninsa da manoma

Baje kolin Kaduna: Kamfanin takin Dangote zai gudanar da shiri tsakaninsa da manoma

  • Ana ci gaba da gudanar da taron baje kolin kasa da kasa a jihar Kaduna, kamfanin Dangote ya halarta
  • Kamfanin takin Dangote ya yi bayani, ya ce zai gudanar da shirin wayar da kai ga manoma da kwastomominsa
  • Gwamnatin Kaduna da ta jihar Kaduna sun yaba wa Dangote bisa jajircewarsa wajen gina tattalin arzikin Najeriya

Kaduna - Wani rahoton Daily Trust ya ce, kamfanin taki na Dangote zai gudanar da shiri na musamman don taimakawa maonma da kwastomomi a yayin bikin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa da za ake gudunarwa a Kaduna.

Shirin na teburin tattaunawa da warware matsalolin kwastomomi da manoma zai gudana ne a yayin bikin baje kolin kamar yadda kamfanin ya bayyana.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya a Ukraine: Aisha Buhari ta mika kokon bara ga Buhari a madadin 'yan Najeriya

Sanarwar da Sashen Sadarwa na kamfanin ya fitar ta ce baya ga kayayyakin takin da ake sayar da su a kan farashi mai sauki tare da fakiti na musamman ga manoma, ana kuma ba da kyaututtuka ga kwastomomi a yayin baje kolin.

Takin Dangote a Kaduna: Za a yi shirin tattaunawa da manoma
Baje kolin Kaduna: Kamfanin takin Dangote zai gudanar da wani shirin manoma a Kaduna | Hoto: businessday.ng
Asali: Getty Images

Da suke bayyana jin dadi da dimbin jari da ayyukan jin kai na rukunin kamfanonin Dangote, shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai masaukin baki gwamnan jihar Kaduna, sun yaba wa shugaban rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote.

Shugaba Buhari ya samu wakilcin Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Hannun Jari, Otunba Niyi Adebayo.

Otunba ya yabawa shirin ne a lokacin da ya ziyarci rumfar Dangote a wajen bikin baje kolin kasuwancin na kasa da kasa karo na 43 da ake gudanarwa a Kaduna, inda ya ce kasa ta yi matukar godiya da irin goyon bayan da Dangote ya basu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Ya bayyana Dangote a matsayin abokinsa saboda irin gudunmawar da yake bayarwa ga tattalin arzikin Najeriya, tallafawa ayyukan gwamnati da na zamantakewa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ribar N1000: Kamfanin BUA ya tona asirin 'yan kasuwa, ya ce sune silar tsadar siminti

A wani rahoton, kamfanin simintin BUA ya ta'allaka ci gaba da hauhawar farashin siminti a kasar ga 'yan kasuwa da ke cin kazamin riba fiye da kima a harkallar siminti a kasar.

Kamfanin ya zargi 'yan kasuwa da taka rawar gani wajen ganin farashin siminti bai sauko ba a Najeriya, lamarin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa a kai.

Shugaban kamfanin, Abdul Samad Rabiu ne ya bayyana haka a lokacin da ya gana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ya ziyartar shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel