Da Dumi-Dumi: Shugaban Rasha zai buɗe tattaunawa da kasar Ukraine

Da Dumi-Dumi: Shugaban Rasha zai buɗe tattaunawa da kasar Ukraine

  • Shugaban kasar Rasha Putin ya amince da tura tawagar gwamnatinsa domin fara tattaunawa da kasar Ukraniya a Minsk
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban ƙasar Ukraine ya bukaci Rasha ta dakatar da sojojinta kuma ta duba yuwuwar tsagaita wuta
  • Rahoto ya nuna cewa dakarun Rasha na cigaba da zagaye babban birnin Ukraniya, sun fara kutsawa ta arewaci

Kafar watsa labarai ta The Cable News ta rahoto cewa kasar Rasha ta shirya tura tawagar wakilai zuwa Belarusian, babban birnin Minsk, domin tattaunawa da kasar Ukraniya.

Wannan na kunshe ne a wani sako da aka karanta daga kakakin Kremlin, Dmitry Peskov, yayin martani kan bukatar shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Za'a fara tattaunawar tsagaita wuta a Minsk
Da Dumi-Dumi: Shugaban Rasha zai buɗe tattaunawa da kasar Ukraine Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wani sashin sakon ya ce:

"Biyo bayan bukatar Zelensky na tattauna wa kan matsayin Ukraniya, Putin zai iya tura wakilai daga ma'aikatar tsaro, ma'aikatar harkokin kasashen waje da gwamnatinsa."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta yiwa kasurgumin mai garkuwa da mutane, Evans, hukuncin daurin rai da rai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wakilan zasu je ne domin tattaunawa da tawagar wakilan ƙasar ta Ukaraniya."

A cewar sanarwan, an zaɓi kasar Minsk a matsayin wurin tattauna wa tsakanin kasashen biyu domin tsagaita wuta.

Ba da jimawa ba, kafar watsa labarai da CNN ta rahoto cewa Ukraniya ta faɗa babbar matsala, yayin da Dakarun Rasha suka saka babban birninta, Kyiv a gaba.

Rahoton ya nuna cewa Sojojin Putin na ƙasar Rasha sun kutsa ta yankin Obolon district dake arewacin Birnin, Mil kaɗan zuwa Cibiyar birnin Kyiv.

Haka zalika sojojin Ukraniya sun yi kokarin maida dakarun Rasha inda suka fito, inda suka tare babbar Gadar Birnin domin dakatar da kwararar sojojin Rasha.

A wani labarin na daban kuma Kotun tarayya ta umarci a ba tsohon AGF dama ya tafi Amurka duba lafiya

Kotun tarayya dake zama a Abuja ta ba da umarnin sakin Fasfon tsohon Antoni Janar domin ya tafi Amurka a duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Dakarun Rasha sun kutsa cikin babban birnin kasar Ukraine, Mutane sun yi takansu

Alkalin Kotun ya umarci Muhammed Adoke, ya tabbata ya dawo da Fasfon cikin kwana uku bayan ya dawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel