Ukraine: Ba Bu Abin Da Zai Faru Da 'Yan Najeriya, Rasha Ta Faɗa Wa FG

Ukraine: Ba Bu Abin Da Zai Faru Da 'Yan Najeriya, Rasha Ta Faɗa Wa FG

  • Jakadan Rasha a Najeriya, Alexei Shebarshin, ya tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa rikicin Rasha da Ukraine ba zai shafi ‘yan Najeriya ba
  • Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya tattauna da jakadan a wata ganawar sirri da suka yi, ya ce Shebarshin ya ce Najeriya kawar Rasha ce
  • Onyeama ya bayyana yadda ya sanar da jakadan Rasha cewa Najeriya ba za ta lamunci cin zarafi daga wata kasar da ke da dangantaka ta jakadanci da ita ba

Abuja - Jakadan kasar Rasha a Najeriya, Alexei Shebarshin, ya tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa ‘yan Najeriya baza su cutu ba a rikicin da ke ta ballewa tsakanin kasar Rasha da Ukraine, The Punch ta ruwaito.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya samu damar ganawar sirri da jakadan ya shaida wa Shebarshin cewa Najeriya kawar Rasha ce.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Ukraine: Ba Bu Abin Da Zai Faru Da 'Yan Najeriya, Rasha Ta Faɗa Wa FG
Ukraine: Ba Bu Abin Da Zai Faru Da 'Yan Najeriya, Rasha Ta Faɗa Wa FG. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

A cewar Onyeama, yayin tattaunawa da Shebarshin ya sanar da shi cewa Najeriya baza ta lamunci cin zarafin kasa da kasa ba daga wata kasar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, kasar da ke da jakada a Najeriya.

Jakadan ya ce Rasha bata kai wa farar hula farmaki

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan ne matsayar gwamnatin tarayya kuma muna da ‘yan Najeriya guda 5,600 a Ukraine kuma hankalin mu a tashe yake musamman ganin bama-baman da ake aunawa Rasha.
“Gwamnatin Najeriya tana shirin zuwa kwaso ‘yan kasar. Ya ce zai yi wa hedkwatar su magana kuma alamu sun nuna cewa suna da alaka mai kyau da Najeriya.”

Kamar yadda NAN ta yanko inda ministan ya ce:

“Jakadan Rasha ya ce baza su bari a cutar da Najeriya ba kuma sojojinsu zasu tabbatar sun kula. Hasali ma ba sa kai farmakin bangaren farar hula.”

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban Rasha zai buɗe tattaunawa da kasar Ukraine

Onyeama ya ce harin ba ya shafar bangaren fararen hulan kasar.

Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Tunda farko, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gana da wakilan kasashen G7 a Najeriya inda ta nuna damuwar ta game da rikicin Rasha da Ukraine tana mai kira da a warware lamarin cikin zaman lafiya, rahoto Daily Trust.

Ministan harkokin kasashen waje, Goeffrey Onyeama, ya gana da wakilan a ranar Juma'a a Abuja, yana mai cewa gwamatin Najeriya ta yi kira da a zauna lafiya kuma a yi amfani da diflomasiyya da wurin warware matsalar cikin lumana.

Onyeama ya ce Najeriya bata goyon bayan matakin da Rasha ta dauka na amfani da karfin soji, tana mai kira ga Rasha ta janye dakarunta, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel