Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu

Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu

  • Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya gana da daliban jiharsa da ke karatu a Ukraine yayin da suke cikin fargabar farmakin da Rasha ta kai kasar
  • Tambuwal ya bayyana cewa tsaron laifiyar daliban na da matukar muhimmanci a gare su, don haka ya ce suna yin duk mai yiwuwa don dawo da su kasar
  • Ya kuma yi kira ga iyaye da su kwantar da hankalinsu kan abubuwan da ke faruwa a Ukraine sakamakon farmakin na Rasha

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa daliban jihar Sokoto na cikin yan Najeriya dubu biyar da ke kasar Ukraine kafin kasar Rasha ta kai masu farmaki.

Yayin da yake zantawa da daliban da ke cikin tashin hankali a Ukraine a jiya Asabar, 26 ga watan Fabrairu, gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, ya sake jadadda cewar gwamnatin jihar na tsare-tsaren da ya dace don kare lafiyar dalibanta da ke karatu a kasar duk da mamayar Rasha.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu
Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu Hoto: The Sun
Asali: UGC

Kwamishinan ilimi na jihar Sokoto, Farfesa Bashir Garba, ne ya yi bayanin haka ga manema labarai, bayan fargabar da ke kara ruruwa tsakanin Rasha da Ukraine, rahoton Independent.

Tambuwal ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Tsaron lafiyar dalibanmu a kasar Ukraine abu ne mai matukar muhimmanci, kuma muna tattaunawa da su akai-akai ta ofishin jakadancin Najeriya amma ba zai yiwu a fara kwashe su daga Ukraine ba saboda a yau sararin samaniyar Ukraine ba shi bai ga tashin jiragen sama."
“Dukka dalibanmu da ke kasar Ukraine suna cikin koshin lafiya kuma muna kokari da jajircewa don dawo da su gida nan ba da dadewa ba da zarar an samar da amintacciyar hanya don zirga-zirgar jiragen sama.
“Don haka muna kira ga iyaye da su kwantar da hankalinsu kan abubuwan da ke faruwa a kasar Ukraine sakamakon farmakin Rasha, gwamnatin jihar na iya bakin kokarinta domin tabbatar da kariya da tsaron lafiyar yaranta da ke karatu a kasashen waje baya ga Ukraine.”

Kara karanta wannan

El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga

Gwamnatin Buhari ta jero iyakoki 4 da 'yan Najeriya za su bi su fita daga Ukraine

A gefe guda, mun ji cewa a ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu, gwamnatin tarayya ta lissafa iyakokin da yan Najeriya da ke tserewa daga yakin Ukraine da Rasha za su iya bi zuwa Poland.

Dakarun sojojin Rasha sun mamaye babbar birnin Ukraine, Kyiv, sannan an kashe mutane da dama tun bayan da aka fara yakin.

Abike Dabire-Erewa, shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna waje, ta bayyana hakan sannan ta sanar da iyakokin da ya kamata yan Najeriya da ke guje ma yakin su bi, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel