Yan bindiga sun farmaki garuruwan Kaduna, sun kashe mutane 7, sun sace mutane masu yawan gaske

Yan bindiga sun farmaki garuruwan Kaduna, sun kashe mutane 7, sun sace mutane masu yawan gaske

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki al'umma a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna
  • Maharan sun halaka mutane bakwai sannan suka yi garkuwa da wasu mutane 57
  • Har ila yau sun harbi wani dalibilin ajin karshe na makarantar sakandaren kimiya da ke Birnin-Gwari, yana kwance a asibiti

Kaduna - Yan bindiga sun kai hare-hare a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, sun kashe akalla mutane bakwai sannan suka yi awon gaba da mutane 57.

An tattaro cewa maharan sun farmaki wata mota a Kuriga, hanyar titin Birnin Gwari zuwa Kaduna a ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa wani dalibin makarantar sakandare ta kimiya da ke Birnin Gwari ya tsere da rauni daga harbin bindiga.

Yan bindiga sun farmaki garuruwan Kaduna, sun kashe mutane 7, sun sace 57
Yan bindiga sun farmaki garuruwan Kaduna, sun kashe mutane 7, sun sace 57 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban kungiyar Birnin Gwari Vanguard for Security and Good Governance, Ibrahim Nagwari, a cikin wani jawabi a ranar Asabar, ya bayyana cewa maharan sun kuma farmaki mazauna a Unguwar Bula, Unguwar Dafillo da Ijinga a karamar hukumar Randagi.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ’Yan Ta’adda Sun Kashe 7, Sun Sace 57, Sun Kuma Jikkata Dalibai Masu Zuwa Rubuta JAMB a Kaduna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Solacebace ta nakalto yana fadin:

“A yau da misalin karfe 10:00 na safe, wani dalibin ajin karshe na makarantar sakandaren kimiya ta Birnin-Gwari ya tsere da raunin harbi a kafadarsa a hanyarsa ta zuwa yin rijistan JAMB/UTME a Kaduna.
“Yan fashin sun bude wuta kan motar da dalibin da sauran mutane ke ciki a kauyen Manini bayan Kuriga a hanyar titin Birnin-Gwari Kaduna.
“Dalibin yana jiran ayi masa tiyata domin cike harsahin daga kafadarsa a babbar asibitin Jibrin Maigwari da ke Birnin-Gwari.
“Hakazalika, yan bindigan sun kashe mutane bakwai a Unguwar Bula, Unguwar Dafillo da Ijinga da ke yankin Randagi, Birnin-Gwari a ranar Asabar.
“Yan bindigar a kan babura kimanin su hamsin sun farkami garuruwan da misalin karfe 11:00 na sadiyar Juma’a sannan suka shafe tsawon awa hudu, inda suka hana mutane yin sallar Juma’a.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

“Yan fashin, baya ga kashe mutane shida a nan take, wani mutum daya ya mutu a safiyar nan a babbar asibitin Jibrin Maigwari, yayin da aka sace wasu 57 wanda da damansu mata ne duk a wannan garin.”

Matsafa sun yi luguden wuta kan masu makoki, sun yi fatali gawar mamacin

A wani labarin, mun ji cewa tashin hankali da hargitsi ya barke a Ebenebe da ke karamar hukumar Awka ta arewa da ke jihar Anambra a ranar Asabar yayin da wasu da ake zargin matsafa ne suka kutsa wurin makoki tare da halaka jama'a.

Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan bindigan sun tsinkayi wurin ne daidai lokacin da aka fito da gawar farfajiyar gidan mamacin.

A wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga jama'ar yankin suna ihu da wayyo yayin da aka yi watsi da gawar a farfajiyar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun dumfaro kauyuka a Filato, hakimai na ta kansu

Asali: Legit.ng

Online view pixel