Da Dumi-Dumi: Babban Jami'in Kwastam da yan bindiga suka harbe ya rasu a Asibiti

Da Dumi-Dumi: Babban Jami'in Kwastam da yan bindiga suka harbe ya rasu a Asibiti

  • Jami'in kwastam da yan bindiga suka bi har gida a Rigachikum, Kaduna suka bindige ya cika a Asibiti
  • Maharan sun farmaki Mohammed Maradun, ɗan asalin jihar Zamfara a gidansa, Likitoci sun yi kokarin su amma rai ya yi halinsa
  • Hukumar kwastam ta tabbatar da faruwar lamarin, kuma tace anjima kaɗan za'a kai gawarsa Zamfara domin masa jana'iza

Kaduna - Yan bindiga sun halaka babban jami'in hukumar Kwastam, Assistant Supretandant Cadree II, Mohammed Maradun, dake aiki a shiyyar B, jihar Kaduna.

Daily Trust ta rahoto cewa yan ta'addan sun farmaki gidansa dake Anguwar Rigachikum, karamar Hukumar Igabi, jihar Kaduna da daren Laraba.

Mutum 6 cikin su harda budurwa da aka sa wa ranar Aure, maharan suka yi garkuwa da su yayin da mamacin ya samu raunin bindiga a harin.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraine: 'Yan majalisun Najeriya za su kwasho daliban Najeriya a Ukraine

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Babban Jami'ai Kwastam da yan bindiga suka harbe ya rasu a Asibiti Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai a halin yanzun, Jami'in gwamnatin tarayyar ya rasa rayuwarsa yayin da Likitoci ke masa tiyata domin ceto rayuwarsa a wani Asibiti da ba'a bayyana ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da muka tuntubi kakakin rundunar FOU na hukumar Kwastam, M. A Magaji, ya tabbatar da rasuwar jami'in da lamarin ya shafa.

Ya bayyana cewa za'a kai gawarsa mahaifarsa dake jihar Zamfara domin yi masa jana'iza da yammacin yau Alhamis.

Magaji ya ce:

"Eh, kuma za'a kai gawarsa gida wurin iyalansa dake jihar Zamfara yau Alhamis."

Yadda lamarin ya auku

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa wasu yan ta'adda sun kai hari yankin Rigachikum da misalin karfe 1:00 na daren ranar Laraba.

Maharan sun kutsa cikin gidajen mutane kuma suka yi awon gaba da mutum shida cikin su har da wata mai suna Khadija, wacce aka sanya wa ranar Aure.

Kara karanta wannan

Buhari ya tafi Nasarawa, Osinbajo ya dura birnin Maiduguri domin wata ziyara

Wani shugaban al'umma a yankin ya shaida mana cewa wannan harin shi ne na farko da aka taɓa kawo musu, kuma sun sanar da yan sanda.

A wani labarin mai kama da wannan Yan bindiga sun yi garkuwa da Amarya ana gab da aurenta da wasu mutum 5 a Kaduna

Wata budurwa mai suna Khadija da ake gab da ɗaura aurenta ta shiga hannun yan bindiga a Rigachikum dake cikin Kaduna.

Wata mata da 'ya'yanta ke cikin waɗan da aka sace, ta ce suna cikin bacci maharan suka shigo, suka tafi da Kadija, waya da Burodi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel