Da Duminsa: ’Yan Ta’adda Sun Kashe 7, Sun Sace 57, Sun Kuma Jikkata Dalibai Masu Zuwa Rubuta JAMB a Kaduna

Da Duminsa: ’Yan Ta’adda Sun Kashe 7, Sun Sace 57, Sun Kuma Jikkata Dalibai Masu Zuwa Rubuta JAMB a Kaduna

Jihar Kaduna - Yan ta'adda sun bindige wani dalibin makarantar sakandare ta kimiyya na Birnin Gwari a Jihar Kaduna da ke shirin rubuta jarrabawar JAMB.

Amma, dalibin ya tsira da raunin bindigan a hanyarsa ta zuwa yin rajistar jarrabawar JAMB, Vanguard ta ruwaito.

Da Duminsa: ’Yan Ta’adda Sun Kashe 7, Sun Sace 57, Sun Kuma Jikkata Dalibai Masu Zuwa Rubuta JAMB a Kaduna
'Yan Ta’adda Sun Kashe 7, Sun Sace 57, Sun Kuma Jikkata Dalibai Masu Zuwa Rubuta JAMB a Kaduna. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Amma, yan ta'addan sun kashe mutanen gari guda bakwai.

Ibrahim Abubakar Nagwari, shugaban kungiyar taro da shugabanci na gari a Birnin Gwari ya nuna damuwarsa kan dawowar rikici a yankin, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a.

Sanarwar da ya fitar ta ce:

"Wasu mutane uku sun tsira raunuka, yayin da aka sace mutum 57."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe

"Matsalar yan bindiga a babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ya tabarbare cikin awanni 24 da suka shude."
"Yau, Asabar, misalin karfe 10 na safe, wani dalibin makarantar sakandare ta kimiyya ta Birnin Gwari ya tsira da harbin bindiga a kafadarsa yayin da ya ke hanyar zuwa rubua jarrabawar JAMB a Kaduna."
"Yan bindigan sun bude wuta a motar da ke dauke da dalibai da wasu a kauyen Manini bayan Kuriga kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna."

Ya cigaba da cewa:

"Yan bindiga sun sace mutum bakwai a Unguwar Bula, Unguwar Dafillo da Ijinga a Birnin Gwari a ranar Asabar.
"Yan bindigan kan babura kimanin su 50 sun kai hari misalin karfe 11 na safiyar Juma'a suka shafe awa 4 suka hana mutane sallar Juma'a."
"Yan bindigan bayan kashe mutum shida nan take, wani kuma ya sake mutuwa da safe a asibitin Jibrin Maigwari, yayin da suka sace mutum 57 mafi yawancinsu mata daga garuruwan."

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Nagwari ya mika godiyarsa ga karamar hukumar bisa biya kudin asibiti na wadanda suka jikkata amma ya yi kira ga gwamnati ta dauki matakin gaggawa na kafa cibiyar JAMB a Birnin Gwari.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel