El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga

El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga

  • Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya koka kan yadda hare-haren yan fashi ke kara kamari a yankin arewa maso yammacin kasar
  • El-Rufai ya ce da shi da wasu gwamnatocin jihohi suna shirin siyo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don taimakawa sojojin sama wajen murkushe 'yan binidiga
  • Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, a yayin tattaunawa da manema labarai a fadar shugaban kasa

Abuja - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya magantu a kan matsalar rashin tsaro da hare-haren yan bindiga da ke kara munana a yankin arewa maso yammacin kasar.

Da yake kokawa kan al’amarin rashin tsaro a Najeriya, El-Rufai ya ce kasar ba ta da isassun jami’an tsaron da za su iya magance al’amarin.

Kara karanta wannan

2023: El-Rufai ya magantu kan kudirin takarar shugaban kasa, ya bayyana wanda zai marawa baya

El-Rufai ya bayyana cewa sakamakon haka ne da shi da wasu gwamnonin jihohi biyar suka yanke shawarar shigowa da na’urorin harba makamai da ake iya sarrafawa daga nesa daga kasar Turkiyya.

El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga
El-Rufai: Ni da wasu gwamnoni 5 za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don murkushe 'yan binidiga Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

A cewar gwamnan, za su aikata hakan ne domin agazawa sojojin saman kasar wajen gamawa da mayakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

El-Rufai ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, a yayin wani taron manema labarai a fadar Shugaban kasar da ke Abuja, BBC Hausa ta rahoto.

“Idan ka gwada mutanen da aka kashe da wadanda aka yi garkuwa da su a 2020 da 2021, abun ya karu sosai. Abin da yasa, wadannan yan ta’addan suna samun kudi da yawa suna sayan makamai, abun ya zama kasuwanci.
“Ba wai ta’addanci bane kawai, ya zama hanya ta tara kudi masu dimbin yawa, don haka sun kara karfi. Amma akwai tsare-tsare da aka yi yanzu da kuma sababbin kayan aiki da sojojinmu suka samu, wanda idan Allah ya yarda za a yi maganinsu.

Kara karanta wannan

Ya kamata a ba mutanen Legas tikitin shiga Aljanna kyauta sabida wahalar cunkoso, inji Malam El-Rufa'i

“Kamar yadda nace inda suke an san su, abun da ya hana kai masu farmaki a wannan shekarar shine rashin damar kiransu yan ta’adda kamar Boko Haram, basu da shugaba daya da sauransu. Amma tunda yanzu kotun tarayya ta ce yan ta’adda ne kamar Boko Haram, sojoji za su iya kashe su, toh za a ga chanji a yan kwanakin nan.
“Akwai karancin jami’an tsaro, kuma ba a samun jami’an tsaro a kwana daya sai an dauke su an yi masu horo, don haka ana shirin daukar jami’an tsaro.
“Sannan gwamnatin Turkiyya tana da wasu na’urori na harbi wanda dama da ni da wasu gwamnatocin jihohi biyar mun yi za mu je Turkiyya za mu zauna da shugabannin kamfanonin kasar mu siyo wadannan mu ba sojojin saman Najeriya domin su yi amfani da su.”

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

Kara karanta wannan

El-Rufai kan batun rashin tsaro: Halin da muke ciki a Arewa maso yamma ya fi na Boko Haram muni

A baya mun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ta’addanci a arewa maso yamma ya fi na rikicin Boko Haram muni duba ga yadda adadin mutanen da ake kashewa da sacewa yake hauhawa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 24 ga watan Fabrairu, yayin tattaunawa da mako-mako da tawagar labarai na fadar shugaban kasa ta shirya a fadar Villa, Abuja, Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana bukatar samar da shiryayyen mafita da kuma mayar da hankali wajen kawo karshen miyagun da ke amfani da kayayyakin aiki da suka fi na rundunonin tsaronmu inganci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel