Da duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa masu saka kuri'a wuta, sun halaka 5

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa masu saka kuri'a wuta, sun halaka 5

  • A kalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai rumfunan zabe
  • An gano cewa miyagun sun budewa jama'a wuta a yayin da suka fito zabe a gunduma ta uku da ke karamar hukumar Enugu ta kudu
  • Ganau ya sanar da yadda suka dinga jiyo muryoyin 'yan bindigan yayin da suke daga muryar cewa sun hana jama'a fitowa zabe

Enugu - Kimanin mutane biyar sun rasa rayukan su a lokacin da 'yan bindiga suka kai farmaki a wuraren zabe guda biyu yayin gudanar da zaben karamar hukumar jihar Enugu a ranar Laraba.

'Yan bindigan sun auka wa akwatin zabe a gunduma ta uku dake karamar hukumar Enugu ta kudu da wani akwatin zaben dake Akpugo cikin Nkanu dake karamar ta karamar hukumar ta yamma, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Bama-baman' da yan bindiga suka ɗana sun tashi da rayukan dandazon Mutane a jihar Neja

Da duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa masu saka kuri'a wuta, sun halaka 5
Da duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa masu saka kuri'a wuta, sun halaka 5. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

'Yan bindigan sun hargitsa wurin, ta hanyar lalata kayayyakin zabe bayan fattatakar masu zaben.

Bayan halaka matanen da suka yi, wasu sun samu raunuka, yayin da suka bankawa ababen hawa wuta, Daily Trust ta ruwaito.

Ganau, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bada labarin yadda aka jiyo 'yan bindigan suna daga murya gami da jan kunne a kan yadda suka haramta zabe a kowanne sashi na kudu maso gabas.

Haka zalika, an samu labarin yadda aka kai wa gidan rediyon jihar Enugu (ESBS) farmaki a Obeagu.

Tawagar manema labaran ta hada da; direba, mai daukar hoto da manema labarai uku da kuma wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN).

Wakilan ESBS guda biyu - Chiamaka Ezeaputa da Chigozie Alex - Nwafor - tare da direba, Ebuka Collins Oghozor, sun sumu damar kubce wa.

Kara karanta wannan

Yan bindigar da suka sace kansila a Sokoto sun nemi a biya kudin fansa miliyan N60

Wani ma'aikacin NAN, wanda ba ya so a ambaci sunanshi, ya tabbatar da yadda wani ma'aikacin su ya tafka hatsari, inda ya siffanta hakan a matsayin "abin jimami da takaici."

Yawan ababen hawa da suka babbake a wurare daban-daban a harabar wurin da yayi kama da wurin zabe, ana cigaba da bincike.

'Yan ta'adda sun toshe titin Yawuri zuwa Koko, sun sheke rai 3 a farmakin

A wani labari na daban, a ranar Asabar, 'yan bindiga sun tare titin birnin Yauri zuwa karamar hukumar Koko dake jihar Kebbi.

Ganau daga birnin Yauri mai suna Umar Bachelor, ya shaida wa Vanguard ta waya yadda 'yan bindiga daga Rijau cikin jihar Neja suka tare titin birnin Yauri zuwa Koko, inda suka halaka a kalla mutane uku da ke taso daga jihar Neja zuwa Sakkwoto, a cewar sa 'yan bindigan sun sheke direba da mutane biyu.

Kara karanta wannan

An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18

Ya bayyana yadda lamarin ya dauki tsawon awa daya, ba tare da dakatarwa ba, Vanguard ta ruwaito.

"Sun tare titin, sannan suka ci karen su ba babbaka na tsawon awa daya, inda suka tafi da kansu ba tare da tuhuma ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel