'Yan ta'adda sun toshe titin Yawuri zuwa Koko, sun sheke rai 3 a farmakin

'Yan ta'adda sun toshe titin Yawuri zuwa Koko, sun sheke rai 3 a farmakin

  • 'Yan ta'adda a ranar Asabar tun tare babban titin Yawuri zuwa Koko inda suka dinga barin wuta har suka halaka rayuka 3
  • An gano cewa, 'yan ta'addan sun fito ne daga Rijau a jihar Neja kuma suka tare masu tafiya daga Neja zuwa Sokoto
  • Ganau ya bayar da labarin yadda suka yi sa'a daya suna cin karensu babu babbaka kuma suka shiga kauyen Shanga inda suka saci shanu

Kebbi - A ranar Asabar, 'yan bindiga sun tare titin birnin Yauri zuwa karamar hukumar Koko dake jihar Kebbi.

Ganau daga birnin Yauri mai suna Umar Bachelor, ya shaida wa Vanguard ta waya yadda 'yan bindiga daga Rijau cikin jihar Neja suka tare titin birnin Yauri zuwa Koko, inda suka halaka a kalla mutane uku da ke taso daga jihar Neja zuwa Sakkwoto, a cewar sa 'yan bindigan sun sheke direba da mutane biyu.

Kara karanta wannan

An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18

'Yan ta'adda sun toshe titin Yawuri zuwa Koko, sun sheke rai 3 a farmakin
'Yan ta'adda sun toshe titin Yawuri zuwa Koko, sun sheke rai 3 a farmakin. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya bayyana yadda lamarin ya dauki tsawon awa daya, ba tare da dakatarwa ba, Vanguard ta ruwaito.

"Sun tare titin, sannan suka ci karen su ba babbaka na tsawon awa daya, inda suka tafi da kansu ba tare da tuhuma ba."

Ya kara da bada labarin yadda da farko suka kai hari cikin Shanga a wani kauye Kwalanga, inda suka yi nasarar sace shanun da ba a san adadi ba, kafin su tare titin Yauri, wanda yayi sanadin mutuwar matafiya uku.

An yi kokarin tuntubar kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, sai dai bai daga wayar ba, kuma bai bada amsar sakon da aka tura mishi ba har zuwa lokacin da aka shigar da rahoton.

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto mutum 7 da dabbobi 142

Kara karanta wannan

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

A wani labari na daban, a ranar Laraba, tawagar 'yan sanda sun yi nasarar dakile farmakin 'yan ta'adda masu yawa, wadanda ke tare mutane su yi musu fashi a titin Zango zuwa Kankara cikin jihar Katsina, Vanguard ta ruwaito.

An samu labarin yadda DPOn Kankara ya jagoranci tawagar 'yan sanda wajen luguden wuta ga 'yan ta'adda yayin raka mutanen da ke wuce wa babban titin tare da kadarorin su, inda suka shake daya daga cikin su, bayan sun gano wani mashin na tserewa daga gare su.

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a kan hakan a hedkwatar su a ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel