Ba A Fahimci Ni Bane Da Na Ce ‘Na Shirya Ƙazamin Artabu Da Kowa’, Tinubu Ya Yi Ƙarin Haske

Ba A Fahimci Ni Bane Da Na Ce ‘Na Shirya Ƙazamin Artabu Da Kowa’, Tinubu Ya Yi Ƙarin Haske

  • Bola Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas, ya ce kafafen sada zumunta sun sauya masa maganar sa wacce ya ce ‘a shirye yake da ya yi komai’ don burinsa na zama shugaban kasa ya tabbata
  • Hadimin Tinubu na harkokin kafafen sada zumunta, Tunde Rahman ne ya bayyana hakan ta wata takarda wacce ya saki a ranar Litinin, inda ya ce ya yi amfani da karin maganan da ke cewa idan zaka yi dambe da alade sai ka shirya yin datti
  • Takardar ta kara da cewa an sauya wa jagoran APC din maganarsa, wacce ya ce ya lashi takobin yin kaca-kaca da duk wanda ke neman dakatar da cikar burin sa na takarar shugaban kasa a 2023

Tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu ya yi fashin baki dangane da maganarsa sa aka sauya wacce ya ce a shirye ya ke da ya yi komai don burinsa na hawa kujerar shugaban kasa ya tabbata, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Na shirya kazamin artabu da kowa, babu abinda zai razana ni, Tinubu

Kamar yadda hadiminsa na harkokin kafafen sada zumunta, Tunde Rahman ya bayyana, ya ce an sauya maganar Tinubu, kuma ya yi maganar ne ga wasu da suke sukarsa sa.

Ba A Fahimci Ni Bane Da Na Ce ‘Na Shirya Ƙazamin Artabu Da Kowa’, Tinubu Ya Yi Ƙarin Haske
Ba A Fahimci Ni Bane Da Na Ce ‘Na Shirya Ƙazamin Artabu Da Kowa’, Tinubu Ya Yi Ƙarin Bayani. Hoto: Premium Times
Asali: Depositphotos

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya mayar da martanin ne yayin da ya yi amfani karin maganar da ke cewa “idan kana son ka yi dambe da alade sai ka shirya yin datti.”

NAN ta bayyana yadda a ranar Lahadi Tinubu ya kai wa sabon Olubadan, Lekan Balogun, ziyara a Ibadan don sanar da shi kudirinsa na takara.

Takardar ta bayana yadda jagoran APC din ya nuna yadda aka sauya masa maganarsa inda yace ya lashi takobin fada kaca-kaca da duk mai yunkurin dakatar da burinsa na shugabancin kasa a 2023.

An sauya maganarsa gabadaya

A cewarsa:

“Rahoton ba daidai bane kuma akwai kuskure a cikinsa. Abin ban takaici shi ne yadda ‘yan jaridu da jama’a suka dinga caccaka suna suka ta.

Kara karanta wannan

Muna hanyar zuwa Kebbi daurin aure aka ce yan bindiga sun tare hanya, Shehu Sani

“Abin ban takaici ne maganganun sa aka dinga saboda an sauya magana ta. Hakan yasa na yi wannan karin bayanin.”

Tinubu ya ci gaba da cewa yayin da ya kai ziyarar, a cikin jawabinsa ko sau daya bai bayyana shirinsa na yin komai don ya tabbatar da kudirin sa ba.

Premium Times ta bayyana yadda Tinubu yace sai da ya natsu kuma ya kula da harshensa sannan ya yi jawabin don gudun jama’a su sauya masa magana amma duk da haka sai da aka samu masu tsegunguma a kafafen sada zumunta.

Ya yi karin bayani akan jawabin Tinubu wanda ya yi a fadar Olubadan

Ya ci gaba da cewa:

“Don karin bayani, lokacin da Tinubu ya je fadar Olubadan cewa ya yi: ‘Barkanku dai. Na zo ne don in roki arziki a wurin ku akan nema min goyon bayan Yarabawa da mutanen kasar nan.
“Na fito takarar shugaban kasan Najeriya ne, kuma akwai wani karin magana wanda yace idan kana shirin kokuwa da alade ka shirya yin datti da kashi.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

“A shirye na ke da inyi datti, babu razanarwa ko kuma zagin da zai bata min rai har yasa in fasa takarar, ko kuma in ce na hakura.”

Takardar ta Tinubu ta bukaci jama’a akan su kasance masu adalci kuma kada su bari su dinga yin kamfen ga wasu dugunzumammun ‘yan siyasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel