Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

  • Sarkin hausawan Anguwar azara da ke Jere, Malam Ibrahim Tanko, ya sanar da cewa yana shirin aurar da 'ya'yansa mata 2 daga cikin hudu da aka sace
  • Tanko ya sanar da cewa ya samu kira miyagun da suka sace iyalinsa amma kawai tambayarsa lambobin sirri wadanda ya rufe wayoyinsa da suka tafi da su
  • A cewarsa, ya tsere ta kofar baya ta gidansa amma bai dauak wayarsa ko daya ba, ya na kuma jiran kiran miyagun a halin yanzu

Kano - Malam Ibrahim Tanko, wani basarake a jihar Kaduna, wanda aka yi garkuwa da yaran shi mata guda hudu da matar shi, ya ce ana shirye-shiryen aurar da biyu daga cikin yaran a ranar 12 ga watan Maris na 2022.

Daily Trust ta ruwaito yadda a ranar Laraba, 'yan bindiga suka auka gidan Tanko, wanda shine Sarkin Hausawan Anguwar Azara cikin yankin Jere dake jihar Kaduna.

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake
Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Tanko yayin zantawa da wakilin Daily Trust ta waya a ranar Asabar, ya bayyana yadda yake shirye-shiryen auran, yayin da 'yan bindiga suka kai musu farmaki.

Da aka tambaye shi ko sun kira sun nemi kudin fansa, ya ce 'yan bindigan sun tuntube shi a ranar Alhamis amma a kan wani abu daban.

Ya ce, sun kira ne suna bukatar mukullin sirrin wayoyin shi guda biyu da suka tafi dasu.

"Maganar gaskiya, lokacin da nayi nasarar tsere wa ta daya daga cikin kofofin gida na, banyi tunanin daukar wayoyi na ba. 'Yan bindigan sun tafi da wayoyi na. Sun kira ni a ranar Alhamis, inda suka bukaci in fada musu lambobin sirrin wayoyin nawa," a cewarsa.

Sarkin Hausawan ya ce, tun lokacin da ya fada musu lambobin sirrin wayoyin nashi, 'yan bindigan basu kara kiran shi ba.

"Amma ina sa ran ganin kiran su, don sanin abinda za su ce, duk da ina rokon jami'an tsaro da su taimaka wajen ceto mata ta da yarana mata guda hudu dake hannun 'yan bindigan," a cewarsa.

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

A wani labari na daban, wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne, sun kai hari majami'ar katolikan da ke Chawai a karamar hukumar Kaurun jihar Kaduna a daren Lahadi.

A farmakin ne suka yi garkuwa da wani malamin addinin kirista bayan sun hallaka daya daga cikin ma'aikatansa.

Vanguard ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun yi garkuwa da fasto Joseph Shekari, amma ba su bar wani mai girkin gidan da ransa ba, wanda har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, inda suka hallaka shi yayin kai harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel