Yan sanda sun dakile mummunan harin yan bindiga a kan hanyar Kaduna-Abuja

Yan sanda sun dakile mummunan harin yan bindiga a kan hanyar Kaduna-Abuja

  • Tawagar yan bindiga da suka yi yunkurin kai hari sun kwashi kashin su a hannun yan sanda a kan hanyar Kaduna-Abuja
  • Kakakin yan sandan Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce yan sanda sun dakile nufin yan bindiga, sun kwato makamai
  • Hukumar yan sanda ta yi kira ga mutanen dake yankin su kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbin bindiga ga jami'an tsaro mafi kusa

Kaduna - Dakarun hukumar yan sanda sun dakile harin wasu da ake zargin yan ta'adda ne a wani kauye dake kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin hukumar yan sandan Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya fitar, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

A cewar kakakin yan sandan, jami'ai sun kai ɗauki ne kan rahoton fasaha da suka samu, inda suka ga yan bindigan adadi mai yawa a kusa da ƙauyen Kurmin Kare dake kan hanyar Abuja-Kaduna a karamar hukumar Chikun.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Bama-baman' da yan bindiga suka ɗana sun tashi da rayukan dandazon Mutane a jihar Neja

Yan sanda a Kaduna
Yan sanda sun dakile mummunan harin yan bindiga a kan hanyar Kaduna-Abuja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce yan ta'addan sun taho da nufin aiwatar da wani mummunan nufin su zuwa wani wuri da ba'a sani ba, amma yan sanda suka fatattake su da karfin tsiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an yan sanda karkashin jagorancin DPO na Kateri, bayan samun bayanai suka ɗugunzuma kuma suka samu nasarar dakile nufin su.

Bayan musayar wuta tsakanin su, bisa tilas yan ta'addan suka tsere kuma suka fasa aiwatar da mummunan nufin su.

DSP Jalige ya kara da bayyana cewa dakaru sun kwato bindiga kirar AK-47 maƙare da alburusai 10, da kuma Harsasan bindiga da yawan gaske.

Guardian ta rahoto Ya ce:

"Jami'ai sun samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 maƙare da alburusai da kuma jakar harsasai daga hannun yan ta'addan."

Wane mataki aka dauka kan yan bindigan da suka tsere?

Kasancewar da yawan yan bindigan sun gudu da raunin bindiga a jikinsu, kakakin yan sandan ya yi bayanin cewa jami'ai na cigaba da kokarin binciko su domin damke su da hukunta su.

Kara karanta wannan

An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18

Bisa haka hukumar yan sanda ta yi kira ga kauyukan dake makwaftaka da yankin su gaggauta kai rahoton duk wanda suka gani da raunin bindiga.

A wani labarin na daban kuma Mayakan ISWAP sun mamaye sansanin sojojin Najeriya a jihar Borno

Yan ta'addan ISWAP sun kai hari sansanin sojojin Najeriya dake Gamboru-Ngala, a jihar Borno domin ɗaukar fansa.

Wani luguden wuta ta sama da sojojin suka kaddamar kan yan ta'addan ya halaka manyan kusoshin kwamandojin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel