Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto mutum 7 da dabbobi 142

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto mutum 7 da dabbobi 142

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda 2 masu tsayawa kan tituna suna yi wa matafiya fashi
  • 'Yan sandan karkashin jagorancin DPOn Kankara, sun yi nasarar fatattakar miyagun da ke tsayawa a titin Zango zuwa Kankara a Katsina
  • Ba a nan suka tsaya ba, sun samu nasarar ceto mutum 7 da suka hada da mata da jariransu kuma sun kwato dabbobi 142

Katsina - A ranar Laraba, tawagar 'yan sanda sun yi nasarar dakile farmakin 'yan ta'adda masu yawa, wadanda ke tare mutane su yi musu fashi a titin Zango zuwa Kankara cikin jihar Katsina, Vanguard ta ruwaito.

An samu labarin yadda DPOn Kankara ya jagoranci tawagar 'yan sanda wajen luguden wuta ga 'yan ta'adda yayin raka mutanen da ke wuce wa babban titin tare da kadarorin su, inda suka shake daya daga cikin su, bayan sun gano wani mashin na tserewa daga gare su.

Kara karanta wannan

Bayan shakatawa da yarinya, wani dan jihar Ribas ya cika a dakin Otal jiya Laraba

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto mutum 7 da dabbobi 142
Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto mutum 7 da dabbobi 142. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a kan hakan a hedkwatar su a ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito.

A kalaman shi:

"DPOn Kankara ya jagoranci tawagar 'yan sanda zuwa titin dake tsakanin Kankara da Zango, bayan samun rahoton yadda 'yan ta'addan suka tare titin, yayin da suke raka mutane da kadarorin su.
"'Yan sandan sun yi nasarar dakile farmakin hatsabiban bayan wata luguden wuta da suka yi musu.
"Sun yi nasarar sheke dan bindigan guda daya, sannan suka gano wani mashin na tsere mara rijista na dan ta'addan, wanda aka fi sani da Boxer."

Haka zalika, DPOn Kankara ya jagoranci tawagar 'yan sanda wajen dakile farmakin 'yan ta'addan dake addabar kauyen Fuloti da Gandu Karfi a karamar hukumar Malumfashi bayan samun kiran gaggawa daga mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Yadda IGP da Marwa suka gana, suka shirya yadda za a damke Abba Kyari da mukarrabansa

Bayan musayar wuta da 'yan ta'addan, 'yan sandan sun yi nasarar sheke daya daga cikin hatsabiban, bayan sun ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da yara da mata masu shayarwa guda hudu.

A wani labari mai kama da hakan, 'yan sandan sun gano bindiga kirar AK-47 guda daya, shanu 82, raguna 70 da babur guda daya, wanda ake wa lakabi da Boko Haram daga hannun hatsabiban da suka auka wa yankunan biyu a ranar Laraba.

Kamar yadda kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya bayyana, bayan sun samu kiran gaggawa game da harin, DPO Kankara ya jagoranci tawagar 'yan sanda wajen dakile hatsabiban a wani guri kusa inda ake kira da Zurunkutun, yayin tsallaka titin Kankara zuwa Sheme.

"Tawagar 'yan sanda sun tasar wa 'yan bindigan ne, yayin wata luguden wuta inda suka yi nasarar sheke daya daga cikin su, kuma suka ceto mata hudu da jinjirayen su. Haka zalika, sun gano wata bindiga kirar AK-47, shanu 82 da raguna 70," yace.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun farmaki sabuwar kasuwar shanu a jihar Abia, sun kashe mutane da dama

Katsina: Tirela ta murƙushe fasinjoji 10 da shanu 30, sun halaka har lahira

A wani labari na daban, a safiyar Alhamis, 10 ga watan Fabrairun shekarar 2022, wata tirela dauke da shanu da fasinjoji wadda ta doshi kudu daga Katsina ta kubce a kauyen Gora a karamar hukumar Malumfashi dake jihar Katsina.

Lamarin ya yi sanadiyyar halakar a kalla fasinjoji 10, shanu 30, inda mutane da dama suka samu raunuka, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel