Matafiya sun yi cirko-cirko yayin da masu zanga-zanga suka toshe hanya a Jigawa

Matafiya sun yi cirko-cirko yayin da masu zanga-zanga suka toshe hanya a Jigawa

  • Harkoki sun tsaya cak na wasu awanni yayin da masu zanga-zanga suka toshe hanyar Gwaram-Basirka da ke jihar Jigawa
  • Direbobin manyan motoci ne ke zanga-zanga a kan rufe sananniyar gadar Gwaram da ta hade iyakar Jigawa da jihohin arewa maso gabas na Bauchi, Gombe har zuwa Adamawa da Taraba
  • Gwamnatin jihar dai ta rufe gadar ne domin yin gyara sakamakon lalacewar da ta yi

Jigawa - Zirga-zirgan ababen hawa da sauran harkokin kasuwanci sun tsaya cak na tsawon sa’o’i da dama a ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairu, yayin da masu zanga-zanga suka toshe hanyar Gwaram-Basirka da ke jihar Jigawa.

Sun yi zanga-zangar ne a kan ci gaba da rufe sananniyar gadar Gwaram da ta hade iyakar Jigawa da jihohin arewa maso gabas na Bauchi, Gombe har zuwa Adamawa da Taraba, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Buhari ya gaza: PDP ta nemi Buhari ya sauka daga kejerar ministan mai, ta fadi dalili

Gwamnatin jihar dai ta sanar da rufe gadar ga manyan motoci a watan Agustan shekarar bara duk daga cikin matakan gyara gadar da ta lalace.

Matafiya sun yi cirko-cirko yayin da masu zanga-zanga suka toshe hanya a Jigawa
Matafiya sun yi cirko-cirko yayin da masu zanga-zanga suka toshe hanya a Jigawa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Masu zanga-zangar wadanda yawancinsu matasa ne sun toshe hanyar inda suka hana zirga-zirgan ababen hawa daga bangarorin biyu.

Saboda haka, matafiya masu zuwa jihohin Bauchi da Gombe daga Kano da Jigawa sun shafe sa’o’i da dama a kan hanya.

Sakamakon haka, an tursasa matafiya sauka da dakawa da kafa zuwa daya bangaren don ci gaba da tafiyarsu.

Manufar zanga-zangar

A cewar Daily Trust, abin da ya janyo zanga-zangar shi ne kafa katangar karfe da aka yi a kan gadar don hana manyan motoci da ke bin hanyar wucewa ta gadar.

A cewar daya daga cikin masu zanga-zangar mai suna Baban Fati Direba, a wajen gangamin, sun dauki matakin ne domin yanjo hankalin gwamnati zuwa ga bukatar samar masu da wata hanyar a kusa da gadar.

Kara karanta wannan

Borno: Nakiyar 'yan ta'addan ISWAP ta fashe, ta halaka rayuka 6

Ya ce sakamakon takunkumin da aka sanya a gadar, an samu karancin man fetur a yankin yayin da farashin kayan abinci da sauran kayyaki suka tashi sosai.

Da take magana kan lamarin, gwamnatin jihar ta tabbatar da rufe gadar Gwaram domin yin gagarumin gyara, inda ta bukaci masu ababen hawa da suyi amfani da madadin hanyoyi.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse ta bakin babban sakataren ma’aikatar, Datti Ahmad kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar, Aminu Usman Gumel, ya ce ambaliyar ruwa ta lalata gadojin biyu a shekarar da ta gabata, kuma bayan tantancewar injiniyoyi, gwamnatin jihar ta yanke shawarar rufe gadojin don aiki.

Ya yi bayanin cewa, manyan motoci marasa nauyi da bas za su iya wucewa kan gadar amma an hana manyan motoci masu nauyi wucewa a yanzu don gujewa rugujewar gadar gaba daya da ma tsaron lafiyar masu ababen hawa kafin a fara aikin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

Kwamishinan ya kuma shawarci masu ababen hawa da su yi amfani da wasu hanyoyi domin zirga-zirgar su da na kayayyakinsu.

2023: Shehu Sani ne kaɗai zai iya ceto jihar Kaduna, inji matasa

A wani labari na daban, mun ji cewa yayin da ake fuskantar babban zaɓen gwamna a 2023, matasan kudancin jihar Kaduna sun ayyana goyon bayan su ga Sanata Shehu Sani.

Matasan ƙarƙashin kungiyar SKYGK sun bayyana cewa Sanata Sani ne kaɗai ɗan siyasan da ya rage, da zai iya ceto Kaduna, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ƙungiyar na da rassa a baki ɗaya kananan hukumomin dake kudancin Kaduna, da suka haɗa da, Zango Kataf, Sanga , Kauru , Kaura, Jaba, Kachia, Chikun, Kajuru, Kagarko, Jema’a da Kaduna South.

Asali: Legit.ng

Online view pixel