Borno: Nakiyar 'yan ta'addan ISWAP ta fashe, ta halaka rayuka 6

Borno: Nakiyar 'yan ta'addan ISWAP ta fashe, ta halaka rayuka 6

  • Nakiyar wasu da ake zargin mayakan ta'addanci na ISWAP ne ta fashe, ta halaka rayuka mutum shida inda wasu na daban suka jigata
  • Mummunan lamarin ya auku a ranar Litinin kan hanyar Gamboru-Ngala da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno
  • Al'amarin ya fara ritsawa ne da wata motar daukar kaya, sannan wasu 'yan sa kai biyu da suka je taimako duk sun sheka lahira

Borno - Mutane 6 sun rasa rayukan su a ranar Litinin, baya ga mutane masu tarin yawa da suka samu raunuka, yayin da mayakan ISWAP suka dasa nakiya a hanyar Gamboru-Ngala a karamar hukumar Ngala dake jihar Borno.

Yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata, wani ma'aikacin tallafi ya ce, al'amarin na farko ya ritsa da wata motar daukar kaya, wacce a nan take mutane uku suka rasa rayukan su.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishinan Zamfara Danmaliki ya koka, ya ce ana barazana ga rayuwarsa

Borno: Nakiyar 'yan ta'addan ISWAP ta fashe, ta halaka rayuka 6
Borno: Nakiyar 'yan ta'addan ISWAP ta fashe, ta halaka rayuka 6. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Majiyar ta ce, fashewar nakiyar ta lashe rayukan 'yan sa kai guda biyu, wadanda suka iso wurin don kawo dauki ga wadanda suka samu rauni.

Duk da dai, sojoji da hukumomin 'yan sa kai ba su yi martani game da harin ba, har zuwa lokacin da aka tattara wannan rahoton.

Haka zalika, Channels Television ta tattaro yadda aka shake wani dan hukumar hadin gwuiwan tsoro na farar hula (CJTF) yayin sintiri a babban titin tarayya na Maiduguri zuwa Gamboru- Ngala, inda aka raunata daya.

Gwamna Babagana Zulum, wanda ya sake bude babban titin tarayyar a satin da ya gabata bayan ya dauki tsawon shekaru uku a kulle, ya kwashe tsawon kwana uku da masu komawa a yankunan Gamboru da Wulgo, don raba kayayyakin abinci, kudade da sauran abubuwa ga masu dawowan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

Babban titin Gamboru zuwa Maiduguri ya kai a kalla kilomita 140 (mil 87), wanda shi ne hanyar kasuwanci a lardin, yayin da ya zama mahada da Kamaru dake makwabtaka.

Rashin tsaron da ya dauki tsawon shekaru 12 a Najeriya, ya lashe rayukan mutane sama da dubu, tun shekarar 2009, bayan salwantar da tarin mutane daga barin gidajen su.

Kwana 2 a Gamboru: Zulum da Shettima sun raba wa wadanda suka koma gida kudi da kayan abinci

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Frafesa Babagana Umara Zulum tare da Sanata Kashim Shettima sun ziyarci garin Gamboru da ke karamar hukumar Ngala daga ranar Lahadi zuwa Talata.

Shugabannin sun duba tare da shiga cikin masu raba kayan abinci da sauran kayan tallafi ga mutane 60,813 masu gudun hijira da wadanda suka koma yankin.

Zulum da Sanata Shettima sun yi tafiyar ne da motoci kuma a ranar farko ta tafiyar sun bai wa jama'ar yankin Gamboru da Ngala 55,253 kayan abinci da sauran kayan tallafi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel