2023: Shehu Sani ne kaɗai zai iya ceto jihar Kaduna, inji matasa

2023: Shehu Sani ne kaɗai zai iya ceto jihar Kaduna, inji matasa

  • Matasan kudancin Kaduna sun goyi bayan takarar Sanata Shehu Sani na zama gwamnan Kaduna a shekarar 2023
  • Matasan sun bayyana cewa babu ɗan siyasan da ya rage wanda zai iya ceto jihar daga wannan halin in ba tsohon sanatan ba
  • A cewar matasan ya kamata kowane ɗan asalin Kaduna ya bada gudummuwarsa wajen tabbatar da kudurin Sani

Kaduna - Yayin da ake fuskantar babban zaɓen gwamna a 2023, matasan kudancin jihar Kaduna sun ayyana goyon bayan su ga Sanata Shehu Sani.

Matasan ƙarƙashin kungiyar SKYGK sun bayyana cewa Sanata Sani ne kaɗai ɗan siyasan da ya rage, da zai iya ceto Kaduna, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ƙungiyar na da rassa a baki ɗaya kananan hukumomin dake kudancin Kaduna, da suka haɗa da, Zango Kataf, Sanga , Kauru , Kaura, Jaba, Kachia, Chikun, Kajuru, Kagarko, Jema’a da Kaduna South.

Kara karanta wannan

Ku taimaka ku sake damƙa amanar Najeriya hannun APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

Shehu Sani
2023: Shehu Sani ne kaɗai zai iya ceto jihar Kaduna, inji matasa Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Matasan sun ce Kaduna ta shiga halin ƙaƙanikayin zubar da jini, kuma a yanzun tana bukatar ɗan siyasa mai kwarewa da basira kamar Shehu Sani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsu suna da yaƙinin idan tsohon sanatan ya karɓi mulki zai yi abin da ya dace wajen ceto jihar daga halin da gwamnatin APC ta jefa ta.

Matasan suka ce:

"Mun gudanar da binciken gano jagora mai tausayin Talakawa da zuciya mai kyau ga al'umma, kuma muka gano Shehu Sani ne kaɗai zai yi abin da ya dace ya gyara jahar mu."

Mu haɗa kai mu goya masa baya - Matasa

Matasan sun bayyana haka ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban tawagar, 'Aikin ceto Kaduna,' Mista Bulus Matthew.

Yace suna rokon Al'ummar jihar Kaduna su haɗa karfi da ƙarfe wajen fafutukar yakin neman zabe har su haɗa wa Sani kuri'u Miliyan biyu domin mafarkinsu ya zama gaskiya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da mata, da 'ya'yan babban jami'in gwamnatin Matawalle a Zamfara

Sanarwan ta ce:

"Mun yi Imanin cewa Sanata Shehu Sani, yana da zuciyar taimakon al'ummarsa kuma ya kwatanta haka lokacin da yake majalisa a 2015-2019."
"Wannan aikin ba na wasu tsirarun kungiyoyi ko mutane bane, ya kamata kowa ya fito ya bada gudummuwarsa."

A wani labarin kuma Na hannun daman gwamnan arewa ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga APC

Rikicin jam'iyyar APC reshen jihar Gombe na ƙara kamari, inda lamarin ya fara shafar gwamnatin gwamna Inuwa Yahaya.

Hadimin gwamna mai bada shawara kan harkokin gwamnati, Jijji Gadam ya yi murabus daga muƙaminsa nan take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel