Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

  • Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Neja
  • An tattaro cewa harin wanda suka fara kaddamarwa a yammacin ranar Asabar yana nan yana ci gaba da gudana har yanzu haka
  • Shugaban karamar hukumar Magama, Safiyanu Ibeto, ya tabbatar da hare-haren

Neja - ‘Yan bindiga na ci gaba da kai farmaki a garuruwan Zoma, Yangalo, Masamagu, Atabo da sauran garuruwan da ke makwabtaka a karamar hukumar Magama ta jihar Neja.

Mummunan harin ya tursasa mazauna kauyukan tserewa zuwa garin Kontagora, hedikwatar karamar hukumar Kontagora.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa farmakin wanda suka fara kaiwa a yammacin ranar Alhamis na ci gaba da gudana har yanzu haka, inda aka ce mutane da dama sun mutu sannan an yi garkuwa da wasu da dama.

Kara karanta wannan

An yi jana'izar DPOn yan sandan da yan bindiga suka kashe a Jibia

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa
Yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare wasu garuruwan Neja Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Har ila yau rahoton ya nuna cewa wasu da dama sun jikkata a harin yayin da wasu suka tsere daga gidajensu.

Da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, kakakin rundunar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin sake kira amma zuwa yanzu bai aikata hakan ba.

Sai dai shugaban karamar hukumar Magama, Safiyanu Ibeto, ya tabbatar da hare-haren.

Wasu mazauna kauyukan da suka zanta da Daily Trust a ranar Lahadi, 13 ga watan Fabrairu, sun ce maharani suna ta kai hari tun daga ranar Alhamis ba tare da hukumomin tsaro sun shiga lamarin ba.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Ko da muka fara masu, basu kawo dauki ba. An barmu a hannun yan bindiga.”

Wata dattijuwar mata, Khadijah Abdullahi, ta ce yaranta aurarru mata su biyu wadanda ke da yara biyar da uku na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Jama’a sun tsere daga gidajensu yayin da yan bindiga suka farmaki garuruwan Neja

Wata da ta tsallake rijiya da baya a harin, Safiya Abdullahi, ta ce:

“Da na hango su, sai na gudu na haye kan tsauni. Ban san cewa wasu daga cikinsu sun gan ni ba lokacin da nake boyewa. Na lullube kaina da hijabi. Suna a kan kimanin babura 30. Cikin ikon Allah, sai suka bukaci na gaggauta barin wajen. Ta haka ne na tsira.”

Wani da ya tsere, Shamsudeen Abdulmalik Atabo, ya ce maharani sun fara kai hari a garuruwa uku da misalin 12:00 na rana kuma har zuwa yammacin Asabar suna chan.

Ya ce:

“Matar yayana na cikin wadanda aka yi garkuwa da su. Yanzu haka ina a Kontagora inda nake zama tare da yan uwana.”

Daily Trust ta tattaro cewa har yanzu yan bindigar na nan suna kai hari a Yangalo, babban garin da suka tara dabobbin sata.

Mazauna kauyukan da suka tsere suna samun mafaka a Usubu, wani yanki na Kontagora.

Kara karanta wannan

Gaskiya 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna da Kotu ta ɗaure

Sojojin sun hallaka yan bindiga 20 da suka yi kokarin sake kai harin makarantar Soji NDA

A wani labarin, rundunar Sojin Operation Thunder Strike sun hallaka akalla yan bindiga 20 da suke kokarin kai harin makarantar horar Sojojin Najeriya watau NDA dake jihar Kaduna.

Wani rahoton PR Nigeria ya bayyana cewa yan bindigan, kimanin su 50 kan babura sun durfafi makarantar da yammacin Alhamis, suna kokarin shiga.

Sojojin sun samu nasarar kawar da yan ta'addan ne sakamkon bayanan da suke samu cewa an ga yan bindiga suna rastawa cikin daji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel