Buhari shugaba mai gaskiya ne wanda Ubangiji ya turo, Osinbajo

Buhari shugaba mai gaskiya ne wanda Ubangiji ya turo, Osinbajo

  • Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kwatanta shugaban sa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban da Ubangiji ya turo kuma mai gaskiya
  • Ya yi wannan furucin ne yayin da yake horar da ‘yan Najeriya akan su mayar da hankali wurin bunkasa baiwar da Ubangiji ya ba su, a cewarsa hakan ne babban jari
  • Ya yi wannan bayanin ne yayin da wasu wakilan Kannywood suka kai masa ziyara karkashin wata kungiyar wayar da kai mai suna 13 x 13 wacce Alhaji Dauda Rarara ya jagoranta

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya kwatanta shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya da Ubangiji ya turo, The Sun ta ruwaito.

Osinbajo ya shawarci ‘yan Najeriya akan mayar da hankali wurin bunkasa baiwar da Ubangiji ya ba jama’a inda yace hakan babban jari ne.

Kara karanta wannan

Buhari ya fi galibin matasar da ke sukansa lafiya, Garba Shehu

Buhari shugaba mai gaskiya ne wanda Ubangiji ya turo, Osinbajo
Shugaba Buhari shugaba mai gaskiya ne wanda Ubangiji ya turo, Osinbajo. Hoto: The Sun
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi furucin ne yayin da wakilan wata kungiyar wayar da kai ta Kannywood mai suna 13 x 13 suka kai masa ziyara, wanda shugaban kungiyar, Alhaji Dauda Rarara da kakakin ta, Yakubu Muhammad suka jagoranci ziyarar.

Osinbajo ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su mayar da hankula akan baiwar da Ubangiji ya basu

Kamar yadda hadimin Osinbajo na harkar watsa labaran sa, Laolu Akande ya bayyana a wata takarda, ya ce Osinbajo ya bukaci ‘yan Najeriya su mayar da hankali akan baiwar da suke da shi don babban jari ne wanda duniya zata gani.

Osinbajo ya kira wasu daga cikin mambobin kungiyar kamar yadda The Sun ta bayyana, wadanda suka kai masa ziyara kamar Rabiu Rikadawa, inda ya ce:

“Ina ganin babban abinda Najeriya take da shi shine mutane masu baiwa. Wani lokacin muna kuskuren boye baiwar mu kuma babbar jari ce.”

Kara karanta wannan

IBB ga 'yan siyasa: Kar ku yi wasa da hadin kan 'yan Najeriya

Ya shaida yadda wasu kasashen ba su da ma’adanai sai jama’a masu baiwa iri-iri kuma hakan yana bunkasa tattalin arzikin kasashen.

Ya ce ‘yan fim suna da tasiri kwarai

A cewarsa:

“Idan ka kalli kasar mu, muna da abubuwan ban sha’awa ta ko ina. Amma kuma wuri ne da kullum mutane suke cikin rigima da juna maimakon hada kai wurin tasowa tare.
“Idan ka kalli harkar wasanni da nishadantarwa, manyan abubuwa da suke kawo hadin kai. Don haka wajibi ne muyi amfani da su wurin hada kawunan ‘yan kasa.
“Ina son masana’antar fim, ina jindadin wakoki na ko wanne yare, kuma na tabbatar mutane da dama suna jindadin su. Wani lokacin har kallon bidiyo kake yi kana kwasar nishadi duk da baka fahimtar yaren.”

Ya kara da cewa, in har sako ya isa, ba matsala bane yare. Don haka ‘yan fim da masu harkar nishadi suna da tasiri mai yawa.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Hasalla Bayan Jami’an Tsaro Sun Kange Shi Daga Ganin Osinbajo a Yayinda Ya Ziyarci Jiharsa

Ya ce suna amfanar mutane da dama kuma suna taimako kwarai wanda hakan ne babban jari.

Mun ji dadi da Ubangiji ya azurta mu da Buhari

Osinbajo ya kara da cewa:

“Mun yi sa’a da Ubangiji ya ba mu shugaban kasa jajirtacce irin Buhari. Abinda yasa nace haka Najeriya tana wani hali. Samun mutum wanda zai fahimci hakan kuma ya tafiyar da ita sai an tona.”

Ya ci gaba da yabon Buhari akan yadda yake samun nasarori duk da yadda ta’addancin ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram ya tasa kasar nan a gaba.

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Jonathan Ya Goyi Bayan Gwamnan PDP Ya Zama Shugaban Ƙasa a 2023

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel