Sunaye: Majalisar dattawa ta amince da wasu mutum 9 da Buhari ya nada a hukumomin NPC da NERC

Sunaye: Majalisar dattawa ta amince da wasu mutum 9 da Buhari ya nada a hukumomin NPC da NERC

  • Majalisar dattawa ta tabbatar da mutane biyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a matsayin kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa (NPC)
  • Ta kuma tabbatar da mutane hudu a matsayin kwamishinonin hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC)
  • Hakan ya biyo bayan samun rahotannin kwamitocinta biyu karkashin jagorancin Sanata Ya’u Sahabi Alhaji da Sanata Gabriel Suwam a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu

Majalisar dattawa a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, ta tabbatar da mutane biyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a matsayin kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa (NPC).

Haka kuma, majalisar ta tabbatar da mutane hudu a matsayin kwamishinonin hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC), jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

An tabbatar da su ne bayan samun rahotanni daga kwamitocin majalisa kan kidaya ta kasa da na wutar lantarki.

Sunaye: Majalisar dattawa ta amince da wasu mutum 9 da Buhari ya nada a hukumomin NPC da NERC
Sunaye: Majalisar dattawa ta amince da wasu mutum 9 da Buhari ya nada a hukumomin NPC da NERC Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Sanata Ya’u Sahabi Alhaji (Zamfara ta arewa) da Sanata Gabriel Suwam wadanda ke jagorantar kwamitocin ne suka gabatar da rahotannin.

An tabbatar da mutanen ne bayan majalisar ta duba rahotannin, rahoton Daily Nigerian.

Sunayen kwamishinonin NPC

Wadanda aka tabbatar da a matsayin kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa sun hada da:

1. Cif Engr. Benedict Ukpong Effiong (Akwa-Ibom)

2. Misis Gloria Fateya Izonfo (Bayelsa)

3. Barr. Kupchi Patricia Ori Iyanya (Benue)

4. Dr. Haliru Bala (Kebbi)

5. Dr. Eyitayo Oyekunle Oyetunji (Oyo).

Sunayen kwamishinonin NERC

Mutane hudu da aka tabbatar a matsayin kwamishinonin hukumar kula da wutar lantarki ta kasa sun hada da:

1. Dakta Yusuf Ali (arewa ta tsakiya)

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

2. Injiniya Chidi Ike (kudu maso gabas)

3. Mista Nathan Rogers Shatti (arewa maso gabas)

4. Mista Dafe Akpeneye (kudu maso kudu).

Hadiman ‘Yan Majalisa sun sanar da Gwamnatin Buhari badakalar da ake yi a Majalisa

A wani labarin, asu fusatattun hadiman ‘yan majalisar tarayya a karkashin Concerned Legislative Aides of 9th Assembly sun gabatar da koke-kokensu ga hukuma.

Jaridar Punch ta ce a ranar Litinin, 14 ga watan Fubrairu 2022, wadannan mukarrabbai suka kai korafi gaban hukumomin bincike na ICPC da kuma EFCC.

Hadiman da suka shirya zanga-zanga a gaban hedikwatocin EFCC da ICPC a garin Abuja sun bukaci a binciki badakalar da ake tafkawa a majalisar kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel