Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Daga dakatarwar da aka yi masa daga hukumar ‘yan sanda har zuwa kama shi bisa zargin alaka da miyagun kwayoyi, labarin DCP Abba Kyari ya zama wani babban abin fade a kasa, lura da irin bajintarsa a baya da yadda rayuwa ta yi masa atishawar tsaki.

Dajarar Kyari ta fara zubewa ne a watan Yulin 2021 lokacin da wata takardar kotu a Amurka ta bankado alakarsa da wani shahararren dan damfara, wato Hushpuppi.

Hushpuppi, yana fuskantar tuhumar zamba a Amurka. Takardun kotun sun nuna cewa, hukumar binciken manyan laifuka ta tarayya (FBI) ta tuhumi Kyari da hada baki da Hushpuppi a badakalar dalar Amurka miliyan 1.1.

Abba Kyari: Yadda rayuwa ta sauya masa
Daga jarumi zuwa rago: Rayuwar Abba Kyari a baya da kuma yanzu | Hoto: Abba Kyari
Asali: UGC

Ko da yake Kyari ya musanta zargin, ‘yan sanda sun dakatar da shi yayin da aka kafa kwamitin da zai binciki zargin nasa da hannu wajen zambar.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA ta yiwa IGP martani

A ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu, Abubakar Malami (SAN), babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), ya ce gwamnatin tarayya da gwamnatin Amurka suna tattaunawa kan yiwuwar mika Kyari.

AGF ya kuma ce an tattara dalilai masu ma'ana kan zargin da ake yiwa Kyari.

Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da luguden lebe kan yiwuwar mika Kyari, hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta bankado boyayyar harkallar Kyari a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu.

Sa'o'i kadan bayan sanarwar, 'yan sanda sun sanar da kama shi tare da mika shi a hannun hukumar NDLEA.

Kyari: Sarki ya zama bawa

Kafin a fara tabarbarewar shaharar Kyari da fadawa wulakanci, ya kasance dan sanda mai farin jini a kafafen yada labaran Najeriya, inda ake bayyana shi da "super cop".

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

Sunansa ya shiga bakin ’yan Najeriya da dama a lokacin da ake tsaka da fuskantar barazanar tsaro mai sarkakiya da ta addabi Najeriya.

A 2019, lokacin da yawan sace-sacen jama’a a kan titin Abuja zuwa Kaduna ya tunzura, Kyari da tawagarsa ne aka tura domin magance matsalar.

Majalisar wakilai ta karrama Kyari saboda “fice a aiki”

A watan Yuni 2020, an gayyaci DCP Kyari zuwa zauren majalisar wakilai kuma an karrama shi "saboda kwazonsa da fice a aiki na tsawon shekaru a rundunar 'yan sandan Najeriya".

Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai ya ce karramawar da aka yi wa Kyari ba wai daga ‘yan majalisar ne kadai ba, daga al’ummar Najeriya ne, inji rahoton TheCable.

A kalamansa yayin gabatar da lambar yabo ga Kyari:

“Ba dan abin da suke yi a kowane lokaci ba ne kuma ga kowa ba sai dai ga wadanda suka bambanta kansu a fannonin hidima daban-daban.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: NDLEA Ta Fara Yi Wa Abba Kyari Zafafan Tambayoyi a Ofishinta

“Haka kuma don nuna wa ‘yan Najeriya cewa duk da rashin kyawun martabar ‘yan sandan Najeriya, akwai jami’ai na kwarai a rundunar.
“Wannan ita ce babbar karramawa domin wannan ita ce cibiya daya tilo da dukkan ‘yan Najeriya ke da wakilci. Wannan ba lambar yabo ce daga majalisar wakilai kadai ba sai dai daga daukacin al’ummar Najeriya.”

Silverbird: 'Gwarzon Jarumin Shekara, 2018'

Shekaru biyu gabanin karramawar majalisar wakilai, DCP Kyari ya kasance amintacce kuma gwarzon shekarar 2018 ta Silverbird Communications.

Da yake mika lambar yabo ga Kyari a madadin Silverbird, Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya yabawa DCP da aka dakatar saboda kokarinsa na "tabbatar da kowa ya samu damar yin barci da dare".

Ya kara da cewa:

"Yana da kyau a karrama duk wanda ke ba da gudummawa don tabbatar da cewa mun sami damar yin barci mai kyau. Idan aka yi la’akari da abin da ya aikata, na gode wa Silverbird da ta zabe shi.

Kara karanta wannan

Idan NDLEA ta gama bincike kan Abba Kyari, za'a mika shi ga gwamnatin Amurka

"Abin da muke bukata ke nan a kasar nan, mu karrama wadanda ke aiki, lokaci ya yi da za a daina karrama wadanda ke ruguza kasa."

Aisha Buhari ta karrama Kyari

Haka kuma a shekarar 2018, Uwargidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta karrama DCP Kyari, kamar yadda jaridar TheCabble ta ruwaito.

An ba shi wani allon karramawa, wanda aka rubuta, "don nuna godiya da kuma sanin irin rawar da yake takawa wajen dakile laifuka a Najeriya".

An ba shi lambar yabon ne a Aso Rock, inda aka yaba wa Kyari bisa rawar da ya taka wajen magance wasu manyan matsalolin da suka addabi al’ummar kasar nan.

A yanzu kuma, da alamu darajarsa ta yi kasa, sannan 'yan Najeriya na ci gaba da mamakin yadda batutuwa suka fito kansa, hakazalika ya shiga tarihi.

A wani labarin, Hukumar hana amfani da miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta yi martani da jawabin Sifeto Janar na yan sanda inda yayi kira ga a hukunta jami'an hukumar da suke taimakawa wajen shigo da hodar Iblis Najeriya.

Kara karanta wannan

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

Zaku tuna cewa a ranar Litinin hukumar NDLEA ta garkame dakataccen DCP na yan sanda, Abba Kyari, kan laifin safarar hodar Iblis mai nauyin kilo 25.

Wannan ya biyo bayan damkeshi da hukumar yan sanda tayi kuma ta mikasa tare da sauran yan sandan dake harkallar tare ga hukumar NDLEA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel