Hadiman ‘Yan Majalisa sun sanar da Gwamnatin Buhari badakalar da ake yi a Majalisa

Hadiman ‘Yan Majalisa sun sanar da Gwamnatin Buhari badakalar da ake yi a Majalisa

  • Wasu hadiman ‘Yan Majalisar kasar nan sun shirya zanga-zanga, su na kukan cewa ana zaluntar su
  • Mukarraban Sanatoci da ‘Yan Majalisar sun zargi shugabannin majalisa da cinye masu hakkokinsu
  • Hakan ta sa kungiyar hadiman ta rubuta korafi zuwa ga fadar shugaban kasa, ICPC da EFCC da jami'an tsaro

Abuja - Wasu fusatattun hadiman ‘yan majalisar tarayya a karkashin Concerned Legislative Aides of 9th Assembly sun gabatar da koke-kokensu ga hukuma.

Jaridar Punch ta ce a ranar Litinin, 14 ga watan Fubrairu 2022, wadannan mukarrabbai suka kai korafi gaban hukumomin bincike na ICPC da kuma EFCC.

Hadiman da suka shirya zanga-zanga a gaban hedikwatocin EFCC da ICPC a garin Abuja sun bukaci a binciki badakalar da ake tafkawa a majalisar kasar.

Mukarraban su na zargin cewa Kilaki da sauran shugabannin majalisa su na da hannu wajen karkatar da hakkokin da ya kamata a ce an biya su tun tuni.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

“Mu na zargin shugabannnin majalisa, Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila da Kilaki, Amos Ojo da karkatar da hakkokin da ake ware mana a shekara saboda harkarlar da ake tafkawa a asusun hadiman ‘yan majalisa.”
“Daga cikin kusan kudin DTA 12 da ake biyan hadiman ‘yan majalisa bayan kowane watanni uku, tun watan Yunin 2019 babu wanda aka biya wannan alawus.”
Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

“Haka zalika jagororin majalisa ba su shirya wani horo ba a cikin shekaru biyu da rabi, duk da an ware kudi na wannan aiki a kundin kasafin kudin shekara.”

- Concerned Legislative Aides of the 9th Assembly

A cewar hadiman, ba ayi amfani da wadannan kudi kan abin da ya dace ba, kuma ba a maida su ba.

An rubuta takardar korafi

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Bidiyon yadda dan sanda ya boye yayin da 'yan bindiga suka kai hari

The Headlines ta ce Zebis Kekung da Kingsley Ejekwu suka sa hannu a wannan korafi da aka aikawa shugaban EFCC na kasa, Mista Abdulrasheed Bawa.

Sauran wadanda takarar za ta je hannunsu sun hada da Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma IGP Usman Alkali Baba.

An kuma sanar da shugaban DSS, Magaji Yusuf Bichi, shugaban ICPC watau Farfesa Bolaji Owasanoye da hadimin shugaban kasa, Babajide Omoworare.

Rikicin APC a Osun

A jiya ne aka ji cewa Rauf Aregbesola wanda tun 1999 yake tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fito gaban Duniya ya nuna zai yake shi a zaben jihar Osun.

Tsohon Gwamnan Osun Rauf Aregbesola da mutanensa sun ja layi, za su yaki Bola Tinubu, su hana Gwamnan Gboega Oyetola mai-ci samun tazarce a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel