Abba Kyari: IGP ya bada umarnin rufe dukkan sassan IRT da STS na 'yan sandan Najeriya

Abba Kyari: IGP ya bada umarnin rufe dukkan sassan IRT da STS na 'yan sandan Najeriya

  • Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya yi umarnin rufe dukkan sassan rundunar IRT da STS a fadin kasar nan
  • Alkali Baba ya umarci dukkan jami'ansu da ke fadin kasar nan da su kai kansu hedkwatar 'yan sanda da ke Abuja
  • Wannan sanarwan na zuwa ne washegarin da aka damke dakataccen shugaban IRT, Abba Kyari, da wasu 'yan sanda hudu da zargin safarar miyagun kwayoyi

FCT, Abuja - Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bada umarnin rufe dukkan sassan rundunar binciken sirri na Intelligence Response Team da Special Tactical Squad a fadin kasar nan.

Wannan na zuwa ne bayan damke dakataccen mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban rundunar IRT na 'yan sandan Najeriya, Abba Kyari da wasu sakamakon zarginsu da ake da harkar safarar miyagun kwayoyi, Channels TV ta rahoto.

Abba Kyari: IGP ya bada umarnin rufe dukkan sassan IRT da STS na 'yan sandan Najeriya
Abba Kyari: IGP ya bada umarnin rufe dukkan sassan IRT da STS na 'yan sandan Najeriya. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Dukkan jami'an 'yan sanda da ke sassa a fadin kasar nan an bukaci da su kai kansu hedkwatar hukumar 'yan sanda da ke Abuja domin karin bayani.

Wata majiyar 'yan sandan wacce ta tabbatar wa da Channels TV kan umarnin hukumar, ta ce jami'an sashin za a sake musu wurin aiki a fadin kasar nan.

A watan Yulin 2020, sifeta janar na lokacin, Mohammed Adamu, ya bada umarnin tarwatsa dukkan sassan da sansanin 'yan sanda na IRT da STS inda aka bar sashin rundunar na hedkwatar kadai sakamakon kukan jama'a kan cin zarafin da suke fuskanta daga jami'an.

A yayin jinjinar da kungiyoyi masu zaman kansu suka yi bayan an tarwatsa rundunar, sun ce da yawa daga cikin cin zarafi da cin mutuncin da 'yan sanda ke yi wa mutane, duk jami'an rundunar ne.

Kamar yadda suka ce, hukuncin Sifeta janar din ya zo ne domin tabbatar da cewa jami'an IRT suna aiki karkashin tsananin kular kwamishinonin 'yan sandan jihohi.

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

A wani labari na daban, a ranar Litinin, hedkwatar 'yan sandan Najeriya ta bayyana sunayen wadanda ake zargi da hada kai da DSP Abba Kyari da wasu 'yan sanda hudu wurin shigo da miyagun kwayoyi cikin kasar nan.

Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA a ranar Litinin ta bayyana ta na neman Abba Kyari da tawagarsa, rahoton Premium Times ya bayyana.

'Yan sanda daga bisani sun damke wadanda ake zargi tare da mika su hannun hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyin domin cigaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel