Abba Kyari: Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA ta yiwa IGP martani

Abba Kyari: Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA ta yiwa IGP martani

  • Kakakin hukumar NDLEA ya yi martani bisa kalaman hukumar yan sanda na zargin boye jami'ansu da sukay aiki tare da Abba Kyari
  • Jami'n hukumar ya yi alkawarin cewa ana kammala bincike kan lamarin za'a bayyanawa yan Najeriya

Hukumar hana amfani da miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta yi martani da jawabin Sifeto Janar na yan sanda inda yayi kira ga a hukunta jami'an hukumar da suke taimakawa wajen shigo da hodar Iblis Najeriya.

Zaku tuna cewa a ranar Litinin hukumar NDLEA ta garkame dakataccen DCP na yan sanda, Abba Kyari, kan laifin safarar hodar Iblis mai nauyin kilo 25.

Wannan ya biyo bayan damkeshi da hukumar yan sanda tayi kuma ta mikasa tare da sauran yan sandan dake harkallar tare ga hukumar NDLEA.

NDLEA ta yiwa IGP martani
Abba Kyari: Ba zamu yi rufa-rufa ba, duk wanda ke da hannu zai gurfana: NDLEA ta yiwa IGP martani Hoto: Buba Marwa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Daga Sarki ya zama Bawa: Rayuwar Abba Kyari a baya kadan da kuma yanzu

Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Baba Alkali, ya yi kira ga Shugaban hukumar hana fasa kwabrin muggan kwayoyi, Janar Buba Marwa (mrty) ya damke jami'ansa dake taimakawa masu safarar kwaya tare da Abba Kyari.

Daily Trust ta ruwaito kakakin hukumar, Femi Babafemi, da cewa hukumar ba zata yi wani rufa-rufa ba, ko wanene sai an tona masa asiri.

Yayinda aka tambayesa shin me yasa ba'a ambaci sunayen jami'an NDLEA da sukayi safarar tare da Abba Kyari ba, Babafemi yace hukumar ba zata boye kowa ba.

Yace:

"Bayan yin abinda ya dace, wani irin rufa-rufa zamu yi? Duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci fushin hukuma. Kuma wannan ne ra'ayin Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa."
"Muna fatan yan Najeriya su bar hukumar ta kammala aikinta kuma muna tabbatarwa yan Najeriya cewa zamu bayyana musu sakamakon binciken."

Mu muka kama yan kwaya ba NDLEA ba

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: NDLEA Ta Fara Yi Wa Abba Kyari Zafafan Tambayoyi a Ofishinta

Dazu mun kawo muku rahoto IGP inda yace jami'an yan sanda ne suka kamasu ba jami'an NDLEA ba, jami'an NDLEA sun barsu sun wuce saboda an basu cin hanci.

A cewarsa, masu safarar kwayar na turawa jami'an NDLEA hotunansu kafin su isa tashar jirgin sama, saboda haka suna ganinsu suke barinsu su wuce.

Yace:

"Jami'an NDLEA sun barsu sun wuce saboda tun kafin su isa Akanu Ibiam an turo musu hotunansu, yayinda suke kokarin fita daga tashar jirgin da kwayoyi ne yan sanda suka kamasu."

"Saboda haka, Sifeto Janar na yan sanda ya bukaci Shugaban hukumar hana fasa kwabrin kwayoyi ya tabbatar ya damke jami'an hukumarsa dake hada baki da yan kwayan kuma ya gudanar da bincike."

Asali: Legit.ng

Online view pixel