Yanzu-Yanzu: NDLEA Ta Fara Yi Wa Abba Kyari Zafafan Tambayoyi a Ofishinta

Yanzu-Yanzu: NDLEA Ta Fara Yi Wa Abba Kyari Zafafan Tambayoyi a Ofishinta

  • Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta fara yi wa DCP Abba Kyari da sauran wadanda ake zargi tambayoyi
  • An kama Kyari da sauran mutanen ne bisa zarginsu da safarar miyagun kwayoyi tsakanin kasa da kasa da wasu laifukan masu alaka da kwaya
  • Femi Babafemi, mai magana da yawun hukumar NDLEA, ya ce hukumar ba zata daga wa duk wanda aka samu da laifi kafa ba

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, a ranar Talata ta fara yi wa dakataccen shugaban yan sandan IRT, DCP Abba Kyari tambayoyi kan zarginsa da hannu a safarar miyagun kwayoyi a Brazil-Ethiopia-Nigeria, Vanguard ta ruwaito.

Majiyoyi daga hedkwatar NDLEA sun bayyana cewa jami'an hukumar suna son kammala yi wa Abba Kyari da sauran wadanda ake zargin tambayoyi zuwa ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Abba Kyari: Sunayen manyan 'yan sanda 5 da aka kwamushe tare da mikawa NDLEA

Yanzu-Yanzu: NDLEA Na Yi Wa Abba Kyari Da Sauran Mutum 4 Da Ake Zargi Zafafan Tambayoyi
An fara yi wa Abba Kyari zafafan tambayoyi a ofishin NDLEA. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Wata majiya ta ce bisa bukatar IGP na yan sanda Alkali Baba na cewa a yi bincika idan suna da hannu a safarar miyagun kwayoyin, hukumar ba za ta ragwanta wa duk wani jami'i da aka samu da hannu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya ce:

"Mun bada tabbacin cewa za a bincika komai cikin sanarwar da muka fitar ranar Litinin domin mu tabbatar an kama dukkan wadanda ake zargi da wadanda za a gayyata yayin binciken kuma a karshe za su fuskanci hukunci. Muna maraba da duk wanda ke da bayani."

NDLEA sun yi kokari, abin a yaba: Kungiya ta fadi me ya kamata a yi wa Abba Kyari

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA), a ranar Litinin, ta yabawa hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa bisa yadda ta fifita aiki fiye da son rai da kishin aljihu.

Kara karanta wannan

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

Kungiyar ta yabawa NDLEA karkashin jagorancin shugabanta Buba Marwa, saboda ayyana neman DCP Abba Kyari, bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi, Punch ta ruwaito.

A yau ne sanarwa ta iso Legit.ng Hausa cewa, NDLEA ta ayyana neman Abba Kyari bisa zarginsa da kokarin kulla harkallar safarar miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel