Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m

Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m

  • Yan bindiga sun yi awon gaba da wani jami’in kwastam a karamar hukumar tsafe da ke jihar Zamfara
  • A yanzu haka sun kira iyalan jami'in mai suna Muhammad Hassan Lawal inda suka bukaci su biya naira miliyan 10 a matsayin kudin fansarsa
  • Hakazalika maharan sun yi garkuwa da wasu mata shida a yankin a ranar Lahadi, 13 ga watan Fabrairu

Zamfara - Yan bindigar da suka addabi al’umman karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara sun yi garkuwa da wani jami’in kwastam da wasu mata shida, HumAngle ta rahoto.

An yi garkuwa da jami’in kwastam din mai kula da jihohin Kano da Jigawa, Muhammad Hassan Lawal wanda ya ziyarci iyalinsa a daren ranar Juma’a, 11 ga watan Fabrairu.

A cewar Hassan Tsafe, wani mazaunin kauyen da abun ya faru kan idon sa, maharan sun shafe kimanin mintuna 30 kafin sojojin da aka kira suka iso.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m
Yan bindiga sun yi awon gaba da jami’in kwastam a jihar Zamfara, sun nemi a biya N10m Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Sai dai kuma, sojojin basu yi nasarar gano maharan ba saboda sun riga sun tsere kafin isowarsu, kamar yadda Tsafe ya bayyana.

Wani kanin jami’in da aka sace, Umar Lawal ya shaida wa Channels TV cewa maharan sun kira iyalan sannan sun bukaci naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa.

Ya ce da misalin 12:00 na ranar Asabar, sun bukaci maharan su karbi naira miliyan uku domin su sake shi amma sun ce sam sai dai a biya miliyan 10.

Ya kara da cewar da misalin karfe 1:00 na rana, maharan sun kashe wayarsu kuma tun lokacin ba a same su don jin ta bakinsu ba.

A halin da ake ciki, yan ta’addan sun sake dawowa a daren ranar Lahadi, 13 ga watan Fabrairu, inda suka sace wata uwa, Hajiya Mai Tuwo da diyarta mace.

Kara karanta wannan

Yan bindigan sanye da kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa har lahira

Yan ta’addan sun tsere kafin isowar rundunar hadin gwiwa da ke yankin, kamar yadda suka yi a lokacin da suka sace kwastam din.

Aisha Sani Tsafe, wata mazauniyar yankin, ta bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne cikin kasa da awa daya kuma basu tuntubi iyalan mutanen da suka sace ba.

Ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu ba.

Ana barazana ga rayuwata don na ki yarda a tsige mataimakin gwamna – Dan majalisar Zamfara

A wani labari na daban, dan majalisar dokokin jihar Zamfara, Salihu Usman, ya bayyana cewa ya gudu ya bar jihar saboda barazanar da gwamnatin jihar ke yi masa don ya ki goyon bayan yunkurin tsige mataimakin gwamna.

Mista Usman shine dan majalisa daya tilo da ya rage a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a majalisar bayan dukka sauran sun bi Gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan ta'adda sun sheke liman, wasu 32, sun sace mata da yara kan kin biyan N40m haraji

Dan majalisar ya ki halartan zaman karshe da majalisar ta yi a makon da ya kamata wanda a lokacin ne yan majalisa 18 daga cikin 22 suka jefa kuri’un tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahadi Ali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel