Yan bindiga cikin kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa a Ogun

Yan bindiga cikin kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahararren dan kasuwa a Ogun

  • Yan bindiga da ake zargin yan fashi da makami ne sun bindige wani hamshakin ɗan kasuwa a Gidan man fetur na jahar Ogun
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun zo a cikin kayan sojoji, suka harbe mutumin a kai, sannan suka yi gaba da wasu kuɗaɗe dake cikin motarsa
  • Hukumar yan sanda ta ce lamarin na da alaƙa da fashi da makami, amma a halin yanzun yan sanda na cigaba da bincike

Ogun - Tsagerun yan bindiga sanye da kayan sojojin Najeriya sun halaka ɗan kasuwa, Oso Femi, a karamar hukumar Ifo ta jihar Ogun, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Mahara sun kashe Femi da misalin karfe 10:00 na dare a gidan man fetur da gas dake tashar motar Nitel, yankin karamar hukumar Ifo jahar Ogun ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka mutum 10, sun sace Hakimi a jihar Katsina

Yan bindiga
Yan bindigan cikin kayan sojojin Najeriya sun bindige wani shahrarren dan kasuwa a Ogun Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ɗan mamacin wanda ya bayyana sunansa da Harbee, yace mutanen sanye da kayan sojoji sun mamaye gidan man suka tsorata mutane daga bisani suka bindige Femi a kai, sannan suka tafi da motarsa.

Harbee ya ce daga baya sun gano Motar mamacin Toyota Corola mai lamba EKY903GZ a yankin Obada Oko Abeokuta, ranar Laraba.

Ya ce:

"Baki ɗayansu sun saka kayan sojoji kuma lamarin ya faru da ƙarfe 10:00 na daren ranar Lahadi, dai-dai lokacin da yake shirin tafiya gida."
"Ya yi kokarin guduwa amma suka harbe shi a tsakiyar kai, suka tattara kuɗi da motar shi suka yi awon gaba da su."
"Mun gano motar a Obada Oko, an aje ta a cikin jeji kuma yanzu haka mun kai motar ofishin yan sanda."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

Kakakin rundunar yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, yace da yuwiwar yan fashin sun samu labarin mutumin na ɗauke da wani adadi na kuɗi masu kauri.

Premium Times ta rahoto kakakin yan sandan yace:

"Case ne na fashi da makami kuma hukumar yan sanda na cigaba da bincike. Mun samu rahoton cewa sun zo sanye da kayan sojoji kuma suka kashe mutumin."
"Ina tunanin sun samu bayanai kan mutumin kuma ɗauke da wasu makudan kuɗi, shiyasa suka ɗauke motar da kuɗin ke ciki. Muna cigaba da bincike yanzu haka."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun ƙara kai mummunan hari, sun kashe fitattun Shugabanni 7 a jihar Imo

Aƙalla shugabannin al'umma bakwai yan bindiga suka kashe a yankin Mmahu dake ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema, jihar Imo.

The Cable ta rahoto cewa yan bindiga sun halaka sanannun shugabannin mutane ne yayin da suka farmaki ƙauyen da safiyar Talata.

Kara karanta wannan

Nasara: Yan bindiga sun kwashi kashin su a hannu yayin da suka kai hari Ofishin yan sandan Kogi

Asali: Legit.ng

Online view pixel