Sarkin Musulmi, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Biyu Sun Hallarci Jana’izar Jikan Sardauna Da Aka Yi a Sokoto

Sarkin Musulmi, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Biyu Sun Hallarci Jana’izar Jikan Sardauna Da Aka Yi a Sokoto

  • An samu labari akan yadda Hassan Danbaba mai shekaru 51, wanda ya rike sarautar Magajin Garin Sokoto ya fadi ya mutu a garin Kaduna ranar Asabar da rana
  • Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar, tare da Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna, Aminu Tambuwal na Sokoto da Atiku Bagudu na Kebbi sun je jana’izar
  • Babban Limamin Masallacin Sultan Bello, Muhammad Akwara ne ya ja sallar jana’izar inda ya ce ko wanne rai mamaci ne kuma ya bukaci kowa ya ji tsoron Allah

Sokoto - Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar, tare da Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, Aminu Tambuwal a Jihar Sokoto tare da Atiku Bagudu na Jihar Kebbi suna cikin manyan mutanen da suka halarci jana’izar jikan Sardaunan Sokoto, Hassan Danbaba, a ranar Asabar a garin Sokoto.

Babban limamin masallacin Sultan Bello, Muhammad Akwara, ya ce ko wanne mai rai mamaci ne don haka ya bukaci mutane su kasance masu bin dokokin Allah yayin da suke da rai, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Yadda Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba, Ya Rasu

Sarkin Musulmi, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Biyu Sun Hallarci Jana’izar Jikan Sardauna Da Aka Yi a Sokoto
Gwamnoni 3 da Sarkin Musulmi sun hallarci jana'izar jikan Sardauna a Sokoto. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An birne Danbaba kamar yadda dokar musulunci ta tanadar a Binaci, kusa da fadar Sultan, makabartar iyalan Magajin Gari.

Wamakko ya ce Danbaba mutumin kirki ne

Yayin tsokaci dangane da mutuwar, Aliyu Magatakarda Wamakko, Shugaban Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dattawa, ya bayyana alhinin sa dangane da lamarin.

Wamakko ya kwatanta marigayi Danbaba a matsayin mutumin kirki kuma shugaban gargajiya mai daraja wanda ya kawo cigaba ga masarautar Sokoto da Najeriya gaba daya. A cewarsa, mutuwarsa babbar asara ce ga masarautar Sokoto saboda an yi babban rashi.

Wamakko ya mika sakon ta’aziyyarsa ta kakakinsa, Hassan Sanyinnawal, kamar yadda Premium Times ta ruwaito, inda ya ce Danbaba ya yi rayuwa cike da hidima ga masarautar, Najeriya da jama’a baki daya.

Yadda Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba, Ya Rasu

Kara karanta wannan

An garkame dan majalisar wakilan tarayya kan almundahanar N185m

Tunda farko, kun ji cewa Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Danbaba, Shugaban masu nada sarki na masarautar Sokoto, ya riga mu gidan gaskiya.

Danbaba, ya yanke jiki ya fadi ne a otel dinsa a Kaduna misalin karfe 11.30 na safe. Ya rasu a hanyarsa ta zuwa asibiti a Kaduna, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Daily Trust ta rahoto cewa wani na kusa da iyalansa, Alhaji Buhari Sarkin Tudun Jabo, ya tabbatar da Danbaba ya rasu a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel