'Karin Bayani: Yadda Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba, Ya Rasu

'Karin Bayani: Yadda Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba, Ya Rasu

  • Alhaji Hassan Danbaba, jikan Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, ya rasu a Kaduna yana da shekaru 51
  • Danbaba, wanda shine shugaban masu nadin sarki a masarautar Sokoto ya yanke jiki ya fadi ne da rana a cewar rahotanni
  • Ya rasu, kimanin shekara guda bayan rasuwar mahaifiyarsa, Aishatu, babban yar marigayi Firimiyan na Sokoto, Sir Ahmadu Bello

Kaduna - Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hassan Danbaba, Shugaban masu nada sarki na masarautar Sokoto, ya riga mu gidan gaskiya.

Danbaba, ya yanke jiki ya fadi ne a otel dinsa a Kaduna misalin karfe 11.30 na safe. Ya rasu a hanyarsa ta zuwa asibiti a Kaduna, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Daily Trust ta rahoto cewa wani na kusa da iyalansa, Alhaji Buhari Sarkin Tudun Jabo, ya tabbatar da Danbaba ya rasu a Kaduna bayan gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 game da rayuwar Magajin Garin Sokoto, Hassan Ahmad Danbaba

Yanzu-Yanzu: Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba, Ya Rasu
Allah Ya Yi Wa Jikan Sardauna, Magajin Garin Sokoto, Hassan Danbaba, rasuwa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Ya shaida wa Daily Trust cewa:

"Muna cikin kaduwa, don haka ba zan iya baka cikakken bayani ba a yanzu. Muna shirin kai gawar mamacin ne zuwa Sokoto inda za a masa jana'iza.
"Za a birne shi a garinsu a Sokoto a yau. Wannan babban rashi ne ba kawai ga iyalansa da Jihar Sokoto ba, amma rashi ne ga kasa baki daya."

Yadda Magajin Garin Sokoto ya rasu

Wata majiyar daban ta ce:

"Magajin ya zo Kaduna ne ranar Alhamis domin ya jajantawa Ministan Tsaro, Janar Aliyu Gusau, bisa rasuwar dan uwansa.
"Kamar yadda ya saba, ya sauka a otel dinsa, Stonehedge a birnin Kaduna.
"Gusau da Magajin sun yi shirin su bar Kaduna tare su tafi Abuja a ranar Asabar. Bayan ya yi wanka misalin karfe 11 na safe. Ya saka kaya domin ya tafi wurin Janar Gusau a gidansa.

Kara karanta wannan

EFCC ta damke Yakubu Musa kan laifin damfarar Surukinsa kudi N3m

"Muna shirin tafiya, ya yanke jiki ya fadi. Hadimansa suka taru suka dauke shi suka kama hanyar asibiti nan take. Amma, a hanya sai ya ce ga garinku."

Magajin Garin na cikin manyan yan Najeriya da suka hadu a Legas a makon da ta gabata domin tattaunawa kan yadda za a kawo karshen matsalolin Najeriya gabanin 2023.

Kafin rasuwarsa, Magajin Garin shine Direktan Jaridar THISDAY.

A dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel