An garkame dan majalisar wakilan tarayya kan almundahanar N185m

An garkame dan majalisar wakilan tarayya kan almundahanar N185m

  • Hanarabul Mamba na majalisar dokokin tarayya ya gurfana gaban kuliya kan zargin damfarar wani dan kasuwa
  • An zargi Hanarabul Saleh da amsan milyan 185 don yiwa Ministan Abuja magana kan wani fili a unguwar alfarma
  • Alkali ya dage zama zuwa makon gobe kuma yace a garkame hanarabul a komar hukumar EFCC

Abuja - An gurfanar da wani dan majalisar wakilan tarayya, Gabriel Saleh Zock, ranar Alhamis gaban kotu kan zargin hannu cikin almundahanar makudan miliyoyi 185.

Hanarabul Gabriel ya gurfana ne gaban Alkali Halilu Yusuf a babban kotun birnin tarraya dake ungwuar Maitama Abuja, rahoton TheNation.

Dan majalisan ke wakiltar mazabar Kachia/Kagarko na jihar Kaduna a majalisar wakilan tarayya.

Hanarabul Zock
An garkame dan majalisar wakilan tarayya kan almundahanar N185m Hoto: thenationnews
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Sharif-Aminu ya bukaci kotu tayi watsi da karar da aka shigar kansa

Hukumar yaki da almundahana da rashawa, EFCC, ta gurfanar da shi ne kan zargin damfarar Injinya Adeyemi Kamar na kudi N185m.

Dan majalisan ya yiwa Adeyemi Kamar alkawarin tayashi yiwa Ministan Abuja magana don samun takardar hakkin mallaka (R of O) na dukiyarsa dake unguwar Guzape.

A cikin kotu, Hanarabul Zock ya musanta zargin da ake masa.

Ita kuwa lauyar mai kara, Maryam Aminu Ahmed, ta bukaci kotu ta garkame dan majalisan a kurkuku.

Dan majalisan wanda ke hannun EFCC ya iso kotun ba tare da lauyan kansa ba, sbaoda haka Alkali Halilu ya bukaci wani lauya Adebara Adeniyi ya tsaya masa don ayi zaman yau.

Daga bisani Alkalin ya bukaci hukumar EFCC ta garkame dan majalisan kuma ya dage karar zuwa ranar 16 ga Febrairu don zaman sauraron beli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel