'Karin Bayani: Gobara Ta Tashi a Gidan Sheikh Ahmad Gumi a Kaduna

'Karin Bayani: Gobara Ta Tashi a Gidan Sheikh Ahmad Gumi a Kaduna

  • Gobara ta tashi a wani sashi na gidan babban malamin addinin musulunci, Dr Sheikh Ahmad Mahmud Gumi a Kaduna
  • Bidiyo da hotunan gobarar da suka fito a dandalin sada zumunta sun suna taba rufin gini mai bene guda a gidan malamin
  • Dr Ahmad Gumi ya tabbatar da afkuwar gobarar inda ya ce kaddamarce ta Allah don ba a san sanadinta ba duba da cewa babu wutar lantarki a lokacin

Jihar Kaduna - Gobara ta tashi da gidan shahararren malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi a yau Asabar.

Rahoton da Vanguard ta wallafa ya ce ana can ana kokarin kashe wutan duk da cewa ba a rasa rai ba.

'Karin Bayani: Gobara Ta Tashi a Gidan Sheikh Ahmad Gumi a Kaduna
Gobara Ta Tashi a Wani Sashi Na Gidan Sheikh Ahmad Gumi a Kaduna. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

'Yan jarida ba su samu cikakken bayani ba duba da cewa kowa ya mayar da hankali ne wurin kokarin kashe gobarar da kuma tabbatar da cewa babu wanda ya rasu sakamakon gobarar.

Daily Trust ta rahoto cewa ana amfani da wani bangare na gidan a matsayin makaranta.

Sheikh Gumi ya tabbatar da afkuwar gobarar, ya ce kaddara ce daga Allah

Dr Gumi ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa 'kaddara ce daga Allah'.

"Kaddara ce ta Allah kuma ba a san abin da ya yi sanadin gobarar ba duba da cewa babu wutan lantarki a lokacin da gobarar ta tashi," in ji shi.

Majiyar Legit.ng kuma ta lura cewa an wallafa bidiyon gobarar a shafin Facebook din malamin a yayin da matasa ke kokarin kashe gobarar don kada ta bazu zuwa wasu sassan gidan.

Tsohon Kyaftin din na Soja ya shahara a kafafen labarai saboda zuwa wa'azi da ya ke yi a sansanin 'yan bindiga a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara.

Kara karanta wannan

Al'ajabi: Yadda tsohuwa ta mutu a zaune akan teburi ba a sani ba tsawon shekaru 2

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.

An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel