Al'ajabi: Yadda tsohuwa ta mutu a zaune akan teburi ba a sani ba tsawon shekaru 2

Al'ajabi: Yadda tsohuwa ta mutu a zaune akan teburi ba a sani ba tsawon shekaru 2

  • Marinella Beretta 'yar shekara saba'in ta mutu tsawon shekaru biyu da suka wuce yayin da take zaune a kujera a gidanta, an gano gawar kwanaki kadan da suka wuce
  • Hakan na zuwa ne bayan da jami’an hukumar kashe gobara na yankin da suka zo su daga wata bishiyar da ta fadi a cikin lambun a makon jiya
  • Har yanzu dai likitocin ba su gano musabbabin mutuwar ta ba, amma gwajin da aka yi a gawar ya nuna cewa ta rasu ne a wani lokaci a karshen 2019

Como, Kasar Italiya - An tsinci gawar wata ‘yar kasar Italiya mai suna Marinella Beretta a zaune a wani teburi a gidanta da ke Prestino, kusa da tafkin Como a Arewacin Italiya.

Kafofin yada labaran Italiya na cewa, 'yan sandan Italiya ne suka gano gawar matar mai shekaru 70, inji rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Gidan da aka tsinci gawar mata bayan shekaru biyu da mutuwa
Aj'ajabi: Yadda aka tsinci gawar mata a zaune kan teburi shekaru biyu bayan mutuwarta | Hoto: cnn.com
Asali: UGC

An ce ba ta da dangi da suka rage a raye a halin yanzu kuma makwabta ba su ganta ba tun watan Satumban 2019, kamar yadda Sky News ta rahoto.

Binciken da aka yi na gano gawar ya haifar da kiraye-kirayen a samar da ingantaccen kulawar dattijai a kasar.

An ba da rahoton makwabta sun dauka cewa ta kaura ne a farkon barkewar cutar Korona, wacce ta afkawa Arewacin Italiya a farkon 2020.

Yadda aka gano gawar

Hukumar kashe gobara ta Como ta gano gawarta a ranar Juma’ar da ta gabata, biyo bayan korafin cewa, wata bishiya ta fadi a lambun matar sakamakon yadda ciyayi suka mamaye lambun, kamar yadda jami’in yada labarai na birnin Como, Francesca Manfredi ta tabbatar wa CNN.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje

Ba a san musabbabin mutuwar ta ba amma bisa la’akari da irin rubewar da ta yi, ana kyautata zaton ta rasu ne a karshen shekarar 2019.

'Yan sanda ba su sami komai ba a wurin da ke nuna alamar kashe ta aka yi.

Magajin garin Como Mario Landriscina ya ce dole ne mutuwarta ta zama "abin tunawa".

Ya gayyaci mazauna yankin da su halarci jana'izar ta, wanda har yanzu ba a sanya ranar da za a yi ba.

Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi

A wani labarin, duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan hana mata Musulmi saka Hijabi a wasu makarantu a jihar Karnataka da ke kudancin Indiya.

Hukumomi a kudancin Indiya sun bada umurnin rufe makarantu ranar Talata yayinda zanga-zanga ya barke kan hana dalibai mata Musulmai shiga aji da Hijabi.

Rikicin wanda ya barke a jihar Karnataka ya tada hankulan jama'a saboda cin zarafin da yan addinin Hindu ke yiwa Musulmai karkashin mulkin Firai Minista Narenda Modi.

Kara karanta wannan

Gaskiya 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna da Kotu ta ɗaure

Asali: Legit.ng

Online view pixel