Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

  • Gine-gine cike da kayan abinci masu kimar miliyoyi sun kama da wuta sakamakon wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar Bauchi
  • An gano yadda gobarar ta fara da tsakar daren Laraba inda ta ci gaba da ci har ranar Alhamis kafin mutane da ‘yan kwana-kwana su samu nasarar kashe wutar
  • Duk da dai har yanzu ba a tabbatar da musabbabin gobarar ba amma ana zargin daga wani shago ne ta fara inda aka adana danyun kayan abinci sai aka kawo wutar lantarki

Bauchi - Mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.

An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira
Wuta ta lakume kayan miliyoyin naira a babban kasuwar abinci na Bauchi. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.

Ba a tabbatar da musabbabin gobarar ba

Wani ganau ya shaida wa Vanguard cewa:

“Ba mu san sanadin wutar ba, amma muna kyautata zaton ta fara ci ne bayan an kawo wuta. Kun san kasuwar kayan abinci ce, don haka tartsatsin wuta kadai zai iya rura gobara. Amma fa gaskiya an yi asara.
“Ina fatan ba zai zama sanadin karayar arzikin wasu ba, da fatan za su samu kwarin guiwar danne zuciyoyinsu don rungumar kaddara. Mu na rokon gwamnati ta sa hannu wurin tallafa wa wadanda mummunan lamarin ya ritsa da su.”

Har yanzu ba a tabbatar da yawan asarar da aka tafka ba

Kara karanta wannan

Ba za ta saɓu ba: Za mu hukunta doddani da ke cin zalin jama'ar mu, Gwamnatin Abia

Yayin da Vanguard ta nemi jin ta bakin masu makamai a kasuwar, sun tabbatar da aukuwar gobarar amma ba su bayar da wasu bayanai ba don har yanzu ba a san takamaiman asarar da aka tafka ba.

Gobarar kasuwar Muda Lawal ita ce ta biyu da ta auku a shekarar 2021, baya ga gobarar kasuwar Wunti mai munin gaske da ta auku a farkon shekarar nan.

Mummunan Gobara Ta Laƙume Shaguna 63 a Kasuwar Jihar Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa gobara a ranar Lahadi ta kone a kalla shaguna 63 a kasuwar Tundun Wada da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

An kyautata zaton wutan ta taso ne daga wani shagon siyar da kifi wutar shagon ke da tangarda.

Yayin ziyarar da ya kai wurin da abin ya faru, Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya jajantawa wadanda abin ya shafa ya ce su dauki abin a matsayin kaddara ne daga Allah.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel