Basaraken Najeriya Ya Musanta Cewa Ya Roƙi Gwamna Ya Bashi Tallafin N20m Domin Ya Auri Gimbiyar Kano

Basaraken Najeriya Ya Musanta Cewa Ya Roƙi Gwamna Ya Bashi Tallafin N20m Domin Ya Auri Gimbiyar Kano

  • Fadar Oluwo ta kasar Iwo ta ce Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi bai nemi N20m daga hannun gwamnan Jihar Osun, Gboyega Oyetola ba, don shirin auren diyar sarkin Kano, Ado Bayero
  • Wasikar ta dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani ranar Juma’a wacce ta nuna cewa fadar Oluwo ta kasar Iwo tana bukatar tallafi na kudi don gudanar da auren basaraken
  • A wata takarda ta ranar Juma’a wacce sakataren watsa labaran Oluwo ya saki, Alli Ibrahim ya musanta gabadaya maganar tallafin inda yace batun aure, lamarin sa ne nashi shi kadai

Osun - Fadar Oluwo na kasar Iwo ta ce Oba Abdulrasheed Adewale Akanbi bai bukaci tallafin N20m daga hannun gwamna Gboyega Oyetola ba, don gudanar da auren sa da diyar Sarkin Kano, Ado Bayero, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Al'ajabi: Yadda tsohuwa ta mutu a zaune akan teburi ba a sani ba tsawon shekaru 2

Wata takarda wacce ta dinga yawo a kafafen sada zumunta ranar Juma’a wacce ta nuna fadar Oluwo ta kasar Iwo tana bukatar tallafi na kudi don shagalin auren basaraken ta hassala fadar.

Basaraken Najeriya Ya Musanta Cewa Ya Roki Gwamna N20m Domin Auren Gimbiyar Kano
Oluwa Ya Musanta Cewa Ya Roki Gwamna N20m Domin Auren Gimbiyar Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce duk mai hankali zai gane cewa takardar ta bogi ce

Takardar ta ranar Juma’a wacce sakataren watsa labaran Oluwo, Alli Ibrahim ya saki ta zo kamar haka:

“Muna sanar da kowa cewa ba mu da masaniya dangane da wasikar da fadar Oluwo ta kasar Iwo ya tura tana bukatar tallafin kudi akan auren basaraken.
“Yayin da muke bukatar a sanar da jama’a don su yi wa fadar adalci, muna son mu tabbatar da cewa takardar ta bogi ce kuma ba daga fadar Oluwo ta zo ba.
“Wasikar bata dace da tsarin fadar Oluwo ba, kuma ‘yan jaridan fada ba su da masaniya akan ta. A duk takardun da suka samo asali daga fada, Oluwo yana sa hannu. Sannan har tsarin rubutun ma ba irin na ofis bane.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar PDP ta tafka kasurgumar asara a Majalisa bayan rasa Sanatoci 6 a shekara 1

“Sakataren sa ba ya da ikon ya tura wa gwamnati wani sako ba tare da masaniyar mai martaba ba. Wasu mutane marasa daraja ne suka shirya wasikar duk don su ci mutuncin fadar. Babu wata hidimar aure da ta fi karfin Oluwo.
“Masu yada takardar ma su kiyaye. Sarauniya tana hanyar zuwa amma ba da kudin al’umma za a auro ta ba. Duk wanda ya san abinda yake yi ya kamata ya gane shirme ce takardar.”

Takardar ta nuna cewa sarkin yana bukatar kudi don yin gagarumin bikin

Daily Trust ta ruwaito yadda fadar Oluwo ta saki wannan takardar ne bayan wata takarda ta dinga yawo a kafafen sada zumunta wacce ta nuna basaraken yana bukatar N20m daga gwamnatin jihar don ya auri Gimbiyar Kano.

Hadimin gwamnan na musamman akan harkar sarauta ne ya amshi takardar a maimakon gwamnan mai kwanan wata 8 ga watan Fabrairun 2022 wacce aka tura wa Oyetola.

Kara karanta wannan

Karar kwana: An shiga jimami yayin da matar tsohon mataimakin gwamna ta rasu

Kamar yadda wani bangaren takardar yazo:

“Mai mataba Oba (Dr) Abdulrasheed Adewale Akanbi, Oluwa na kasar Iwo ya ba ni umarnin sanar da kai cewa Oluwo zai auro gimbiya daga masarautar Kano, diyar Ado Bayero. Ina farin cikin sanar da gwamna cewa bikin da zai hada masarautun guda biyu yana bukatar kashe dukiya mai yawan gaske. Hakan yasa muke neman tallafi daga gwamnatin jihar nan.”

Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure

A wani labarin daban, wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.

Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.

Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel