Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure
- Peter Oyuk, tsoho mai shekaru 84 ya bayyana mamakin sa dangane da irin abin da matan sa su ka yi masa
- A cewar tsohon, shekaru 47 kacal kenan da ya yi tafiya ya bar matan sa 2, ba su iya jiran sa ba sai suka sake aure
- Oyuk ya bar iyalan sa a kauyen Makale dake Malava a kasar Kenya, ya yi tafiyar ne a 1974 lokacin ya na da shekaru 37
Kenya - Wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.
Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.
Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.
Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere
Oyuka ya je Kakamega a shekarar 1983, 1992 da 1996, sai dai duk da haka bai taba zuwa wurin iyalansa ba duk da wurin ya yi kusa da su. Bayan kwashe shekaru da dama, matan sa sun cire rai daga tsammani, su ka yi auren su.
A ranar Talata, 21 ga watan Satumban 2021, Oyuka ya koma kauyen sa inda mutane kadan ne su ka gane shi.
Daya daga cikin matan yaran sa ta bukaci jama’a su yi gaggawar kawo dauki saboda tsoron wani mutum ya shigo mu su harabar gida kamar yadda LIB ta ruwaito.
Kamar yadda al’adar Luhyia ta tanadar, sai da suka yanka farar akuya don neman tsarin abinda zai iya zuwa ya dawo sannan aka amince da dawowar sa gidan.
An sanar da shi cewa matan sa sun dade da cire tunanin sa a ran su
Bayan isar sa gida ne aka sanar da shi cewa matan sa sun dade da kara aure da cire tunanin sa daga ran su.
Yayin tattaunawa da manema labarai, Oyuka ya ce ya ji dadin yadda iyalansa suka amince da shi amma ya yi mamakin yadda matan sa ba su iya jiran sa ba.
Kamar yadda ya ce:
“Na so ace mata na su na nan don su amshe ni cikin gidan nan.
“Ina yi wa mata na 2 fatan alheri. Amma ina so su sani cewa ina nan da rai don haka su nemi lokaci su ziyar ce ni."
Bayan tafiyar sa har aure ya sake yi
An samu bayanai akan yadda bayan tafiyar sa ya je Tanzania ya kwashe shekaru 13 a can.
Ba soyayya kadai ya yi da wata mata a Tanzania ba, har haihuwa ya yi da ita.
Bayan zaman sa ya kare a kasar, ya koma Kenya daga nan ya rasa hanyar sadarwa tsakanin su.
Kamar yadda ya bayyana:
“Matata ta Tanzania ta daina ganawa da ni kuma har yanzu ba ta ba ni damar ganin dan mu ba.”
Bayan Oyuka ya koma gida da taimakon wata wallafa da wani mutum ya yi a kafar sada zumunta ta Facebook inda tsohon ya yi bayanai dalla-dalla, daga nan ne har ya isa wurin iyalin sa.
Dan sa mai shekaru 53 wanda ya bari yana da shekaru 6 a duniya ya ga wallafar, ta nan ne ya nemo shi ya mayar da shi gida.
Oyuka ya ce yana ta fama da ciwo kuma kudaden da ya samu bayan wani noman albasa da yayi duk ya kashe su wurin neman magani. Daga nan ne ya yanke shawarar komawa gida.
A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu
A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.
Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.
Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng