Akwai yiwuwar PDP ta tafka kasurgumar asara a Majalisa bayan rasa Sanatoci 6 a shekara 1

Akwai yiwuwar PDP ta tafka kasurgumar asara a Majalisa bayan rasa Sanatoci 6 a shekara 1

  • Alamu su na nuna cewa kafar Sanata Biodun Olujimi ta fara barin Jam’iyyar hamayya ta PDP a Ekiti
  • Watakila Sanatar ta Ekiti ta sauya-sheka bayan ta gaza samun takarar gwamna a jam’iyyar PDP
  • Olujimi ta kafa kwamiti da zai ba ta shawarar matakin da ya kamata ta dauka a tafiyar siyasarta

Ekiti - PDP ta reshen jihar Ekiti ta kama hanyar wargajewa a sakamakon mummunan rikicin gidan da ya kara kamari bayan zaben ‘dan takarar gwamna.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Talata, 8 ga watan Fubrairu 2022 cewa Sanata Biodun Olujimi da mutanenta su na tunanin su tsere daga PDP.

Sanata Olujimi mai wakiltar Ekiti ta kudu ba ta ji dadin sakamakon zaben fitar da ‘dan takarar gwamna da aka shirya ba, inda bangaren Ayo Fayose ya yi galaba.

Kara karanta wannan

Karar kwana: An shiga jimami yayin da matar tsohon mataimakin gwamna ta rasu

‘Yar majalisar ta janye kanta daga cikin masu neman takarar gwamna a PDP, ta na kukan cewa jam’iyyar hamayyar ba ta ganin irin kokarin da take yi a Ekiti.

Za mu dauki mataki - Sanata

Babbar ‘yar siyasar da tarin magoya-bayanta sun ce za su dauki mataki a kan yiwuwar ficewa daga jam’iyya. Nan da ‘yan kwanaki za a ji inda suka sa gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani rahoto da Punch ta fitar dazu ya tabbatar da cewa PDP ta fusata Sanata Biodun Olujimi.

Sanatoci
Biodun Olujimi da wasu Sanatoci a bakin aiki Hoto: @Biodun_olujimi
Asali: Twitter

Kwamitin Tunji Odeyemi

‘Yar siyasar ta ce ta nada kwamiti a karkashin jagorancin tsohon gwamna na rikon kwarya, Tunji Odeyemi domin tuntubar magoya bayanta a fadin jihar Ekiti.

Idan kwamitin ya zauna da ‘yan gani-kashe nin Sanatar, zai bada shawarar abin da ya dace. Akwai alamun da su ke nuna zaman Olujumi ya kare a jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Tsige mataimakin gwamnan Zamfara: Majalisa ta lissafo laifukan Aliyu Gusau

PDP ta yi rashi a Ekiti

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shi ma tsohon gwamna Segun Oni ya bar jam’iyyar PDP a sakamakon zaben fitar da ‘dan takarar da aka shirya a makon jiya.

Rahoton na Premium Times ya ce watakila Injiniya Oni ya shiga APGA domin ya yi takarar gwamna.

Bangaren Fayose ne suka yi galaba a zaben fitar da gwani na jam’iyyar PDP. Hon. Bisi Kolawole ya doke Segun Oni da duk sauran wadanda suke neman tikiti a PDP.

PDP ta na rasa Sanatoci

A jiya ake jin cewa shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya yi wa Emmanuel Bwacha, sanata mai wakiltar Taraba ta kudu, barka da zuwa jam’iyyar APC.

Kafin shi irinsu Sanata Stella Oduah, Sanata Elisha Ishaku Abbo, Peter Nwabaoshi, Lawal Anka da Sahabi Ya'u duk sun tsere daga PDP, sun shiga jam'iyya mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel