Neja: Gwamnati za ta fara bayar da kuɗi ga duk wanda ya kawo bayanan sirri kan 'yan ta'adda

Neja: Gwamnati za ta fara bayar da kuɗi ga duk wanda ya kawo bayanan sirri kan 'yan ta'adda

  • Gwamnatin Jihar Neja ta ce za ta bada kudi ga duk wanda ya kawo bayanan sirri dangane da harkokin ‘yan ta’addan da suka addabi jihar
  • Gwamnatin ta bayyana hakan ne don samar da damar da za ta taimaka wa jami’an tsaro samun bayanan sirri kan masu ta’addanci a jihar
  • Sakatariyar watsa labaran gwamnan, Mary Noel-Berje, ta ce rashin tsaro ya tsananta a jihar har ta kai ga gwamnatin ta dakatar da wasu ayyukan da take yi

Neja - Gwamnatin Jihar Neja ta lashi takobin yi wa duk wanda ya kai bayanan sirri dangane da harkokin ‘yan ta’adda a jiharsa sha-tara ta arziki, The Nation ta ruwaito.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne don samar da damar da za a gano sirrin ‘yan ta’addan don kawo karshen ayyukan su a jihar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Gwamnatin Neja za ta fara biyan kudi ga wadanda za su tona asirin 'yan ta'adda
Gwamnatin Neja za ta fara biyan wadanda za su bata bayanai kan 'yan ta'adda. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Sakatariyar watsa labaran gwamnan, Mary Neol-Berje, ta ce rashin tsaro ya zama babban kalubalen da ya addabi jihar hakan ya sa Gwamna Sani Bello ya kawo wannan tsarin a matsayin mafita.

Gwamnatin ta dakata da wasu ayyukan da take yi saboda ta’addanci

Kamar yadda takardar ta bayyana:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Gwamna Sani-Bello ya kawo wannan mafitar ne don bayar da kafar da zata samar da bayanan sirri ga jami’an tsaron jihar. Gwamnatin jihar, ta kwamishinan harkokin kananun hukumomi da harkokin tsaron cikin jihar, ta sanar da batun bayar da sha-tara ta arziki ga masu kawo bayanan sirri akan ‘yan ta’addan.”

The Nation ta ruwaito yadda Barke ya ce ta’addanci ya janyo tashin hankali da koma-baya wurin aiwatar da wasu ayyuka a jihar.

A cewarsa:

“Wajibi ne mu bayyana yadda harkokin ‘yan ta’adda ya janyo koma-baya ga ayyukan da gwamnatin jihar ya kamata ta aiwatar. Akwai ginin burtalin Bobi na miliyoyin nairori, titina da sauran ayyukan da suka tsaya cak saboda ta’addanci.”

Kara karanta wannan

Gwamnoni da Majalisar Tarayya na neman taba karin albashin da aka yi ta bayan-fage

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel